Ɗauke Sojoji A Garin Gora II: Ana Ta Kai Masu Hari ...An kashe mutun 1, an sace mata 5

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07062025_154241_FB_IMG_1749310857128.jpg

Daga Wakilanmu 
@ Katsina Times 

Kwanakin baya al'ummar garin Gora II da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina suka yi koke ga hukumomi daban-daban a jihar da gwamnatin tarayya cewa sojojin da aka ɗauke a garin sakamakonsa zai zama musiba ga garin Gora da sama da ƙauyuka 20 da ke kewaye da garin da harkokin kasuwanci, noma da karatun yankin baki ɗaya.

Kiraye-kirayen da hukumomi daban-daban na jiha da tarayya suka ce suna duba lamarin, ana cikin wannan yanayin na jiran tsammanin dawo da sojojin, yanzu haka ɓarayin har sun fara kai hare-hare babu ƙaƙkautawa a garin.

A ranar Lahadi 1 ga Yuni, ɓarayin sun shiga garin na Gora II, inda suka tafi da mata huɗu, ta farkonsu sunanta Izzatu Nazifi, matar aure ce tana da 'ya'ya huɗu.

Sai Maryam, ita ma matar aure ce, har da 'ya'ya. Sai Maryam ita ma matar aure ce. Sai Zalihatu Muhammad, matar aure ce mai 'ya'ya biyu.

A kuma ranar Talata 3 ga Mayu ɓarayin suka shigo suka kashe wani matashi mai suna Auwal Bishir, wanda ake kira da Ɗan Auwalu mai sai da waya matashi mai ƙoƙarin nasa na kansa yana da mata da kuma 'ya'ya.

A ranar Talata da suka kashe Ɗan Auwalu a ranar suka tafi da wani magidanci mai suna Alhaji Amadu Gora yana da mata uku da 'ya'ya sun kai 20.

A ranar Laraba 4 ga watan Yuni suka shigo garin su da yawan gaske suka firgita garin suka fita da saƙon za su ƙara dawowa.

Mutanen Gora sun ce ba su taɓa ganin wannan tashin hankali ba tsawon shekaru da sojoji ke ba garin kariya sai yanzu.

Mutanen garin sun yi iyakar ƙoƙarin suna kare garin, amma ɓarayin sun zo da yawa da kuma manyan makamai.

Jaridun Katsina Times sun yi ƙoƙarin jin ta bakin 'yan sanda da rundunar soja, amma ba su yi nasara ba.

Follow Us