Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES | 11 ga Yuni, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta karyata jita-jitar da ke yaduwa cewa an rufe manyan hanyoyi da ke haɗa Dutsinma da 'Yantumaki da Marabar Kankara, bisa hujjar cewa akwai matsalar tsaro a yankin.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, 11 ga Yuni, 2025, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, ya bayyana cewa wannan rahoto ƙarya ne kuma yana da nufin jefa jama’a cikin ruɗani da tashin hankali.
Dr. Zango ya ce babu wani umarni daga gwamnatin jihar ko hukumomin tsaro da ya bayar da sanarwar rufe hanyoyin da aka ambata, yana mai tabbatar da cewa hanyoyin Dutsinma zuwa ‘Yantumaki da Marabar Kankara a buɗe suke kuma amintattu ne ga masu ababen hawa da sauran jama’a.
Rudanin ya samo asali ne daga wata sanarwa da ake zargin Shugaban Ƙungiyar Direbobi ta NURTW reshen Dutsinma, Malam Aminu Usman, ya fitar, inda aka ce an rufe hanyoyin saboda tsanantar matsalar tsaro.
Sai dai, shugabancin NURTW na jihar Katsina ya nesanta kansa daga wannan sanarwar, yana mai bayyana cewa shugaban reshen Dutsinma ya fitar da sanarwar ne ba tare da tuntubar ofishin jiha ko hukumomin gwamnati ba.
Shugaban ƙungiyar NURTW na jihar Katsina, Alhaji Musa Garba Yandoma, ya tabbatar da cewa an dakatar da Malam Aminu Usman daga mukaminsa na shugaban reshe har sai an kammala bincike kan yadda aka fitar da wannan sanarwa da ta janyo rudani.
“Ba mu samu wani umarni daga gwamnati ko jami’an tsaro ba. Matakin da shugaban reshen Dutsinma ya ɗauka ya saba wa ƙa’idar ƙungiya. Bai nemi shawarar kowa ba, kuma hakan ya tayar da hankali a tsakanin al’umma,” in ji Alhaji Yandoma.
A cewar Dr. Zango, duk da cewa akwai ƙalubalen tsaro a wasu yankuna na jihar, rahoton da ya shafi hanyar da ake magana a kai ya wuce gona da iri. Ya ce gwamnati na ci gaba da sanya ido da sanya shingen tsaro a kan hanyar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Rufe wannan hanya zai janyo fargaba da cikas ga harkokin kasuwanci da zamantakewa na al’ummomin da ke dogara da ita. Haka kuma zai iya hana motocin agaji kamar na asibiti da na kashe gobara isa inda ake buƙatar su,” in ji shi.
Gwamnati ta bayyana cewa za a gudanar da bincike mai zurfi kan tushen wannan sanarwa da dalilin da ya janyo ta, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
A ƙarshe, Gwamnatin Jihar Katsina ta bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba, tare da karɓar bayanai daga hukumomin da suka dace kawai.
“Wannan hanya ba kawai hanyar sufuri ba ce, alama ce ta haɗin kai da ci gaban jama’a. Gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi da duk wasu muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar,” in ji Dr. Zango.