KATSINA TIMES
Shugabar hukumar ci gaban ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUDA-NEPAD), Ms. Nardos Bekele-Thomas, ta kai ziyarar aiki a ofishin AUDA-NEPAD na Najeriya da ke Abuja, inda ta samu tarba daga Shugaban Hukumar na ƙasa, Hon. Jabiru Salisu Abdullahi tare da manyan jami'an hukumar.
A yayin ziyarar, shugabannin biyu sun jaddada kudurinsu na ƙarfafa dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren ƙasa da na nahiyar domin hanzarta aiwatar da Ajandar 2063 da kuma Shirin Ayyukan Ƙasa na Najeriya (NPoA). Ms. Bekele-Thomas ta yaba da gudummawar Najeriya ga ci gaban yankin, tare da neman ƙarin haɗin kai domin cimma manufofin ci gaba masu amfani da gamsar da al'umma.
A jawabinta, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da biyan ƙudaden da ta saba warewa ga AUDA, tana mai cewa irin wannan tallafi na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da aiwatar da muhimman shirye-shirye, ciki har da noma, shugabanci nagari, ƙarfin matasa, da tsarin kimanta ayyukan ƙasashe.
A nasa bangaren, Hon. Jabiru Salisu Abdullahi ya tabbatar wa shugabar ta nahiyar da cewa Najeriya za ta ci gaba da mara wa AUDA-NEPAD baya. Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a 'yan kwanakin nan, ciki har da rabon tallafi ga kananan manoma da shirye-shiryen horaswa ga ma’aikata da abokan hulɗa.
Ziyarar ta nuna sabon babi na ƙarfafa dangantaka, inda ɓangarorin biyu suka nuna kwarin gwiwar cimma ingantattun manufofin ci gaba a Najeriya da nahiyar gaba ɗaya.