"Ka Daina Tunanin Komawa Aso-Rock A 2027, Tunda Ba Gidan Gadon Ka Bane" Ƙungiyar Yarbawa ga Bola Tinubu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04082025_214954_FB_IMG_1754344125536.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Ƙungiyar al’adun gargajiya ta Yoruba mai suna (Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá) ta yi kaca-kaca da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana zarginsa da gaza cika alkawuransa da kuma jefa ƙasar cikin mawuyacin hali na tattalin arziki da tsaro.

A wata sanarwa da mai jagorantar ƙungiyar, Olusola Badero, tare da daraktar kungiyar Princess Balogun suka fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta nuna damuwa kan karancin abinci, talauci, da yawaitar yara marasa zuwa makaranta a yankin kudu maso yamma da ma ƙasa baki ɗaya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tsauraran matakan tattalin arziki da faduwar darajar naira sun yi wa miliyoyin 'yan Najeriya zafi, suna lalata kananan masana’antu da jefa mutane cikin yunwa.

Haka kuma, ƙungiyar ta soki yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta, inda ta ba da misalin sace manoma bakwai a ƙaramar hukumar Akure North, Jihar Ondo, da wasu Fulani da ake zargi suka yi.

A cewar sanarwar, ‘yan bindigan sun buƙaci fansar Naira miliyan 100, kafin su rage zuwa Naira miliyan 20, amma daga ƙarshe dangin waɗanda aka sace sun samu tara Naira miliyan 5 da abinci kafin a sake su a Ikere-Ekiti, Jihar Ekiti.

Ƙungiyar ta bayyana cewa Tinubu ya kasa sauke nauyin da ya ɗauka na tabbatar da tsaro da walwala ga ‘yan ƙasa, tana mai cewa “Aso Rock ba gidan gadonsa ba ne,” kuma ya kamata ya daina mafarkin sake tsayawa takara a 2027.

Ta ce maimakon jin daɗi daga mulkinsa, mutanen kudu maso yamma na fuskantar tsoro, cin zarafi, da kuma tsare ‘yan jarida da masu sukar gwamnati don hana su faɗar ra’ayinsu.

Bugu da ƙari, kungiyar ta bayyana cewa lamarin ‘yan bindiga a yankin Kwara ta Kudu musamman a Ifelodun, Irepodun, Isin da Ekiti ya zama abin tsoro, inda Fulani masu bindiga ke addabar al’umma ba tare da wata fargaba ba.

“Najeriya ba ƙasar da babu doka ba ce,” in ji sanarwar. “Shugaba Tinubu bai damu da halin da al’umma ke ciki ba, sai burin siyasar 2027 kawai ya ke yi."

A ƙarshe, ƙungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya daina tunanin sake neman mulki, tana mai cewa ba za su sake ba shi ƙuri’a ba.

Follow Us