Kwamitin yaƙi da cutar ƙarancin abinci mai gina jiki (Malnutrition) da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya kafa ya fara gudanar da ziyarce-ziyarcen asibitoci a fadin jihar domin duba matsalar da kuma gano hanyoyin magance ta.
Kwamitin, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Zakka da Waqafi ta Jihar Katsina, Dakta Ahmad Musa Filin Samji, tare da dukkan mambobinsa, ya kai ziyara a yau Alhamis, 14 ga watan Agusta, zuwa wasu manyan cibiyoyin kiwon lafiya.
Ziyarar ta fara ne a Asibitin Kofar Sauri, inda kwamitin ya samu tarba daga jami’an ƙungiyar MSF – Médecins Sans Frontières. Daga nan kuma, tawagar ta wuce zuwa Asibitin Turai Yar’adua domin ci gaba da aikin tantance matsaloli da tattaunawa da jami’an lafiya.
Dakta Ahmad ya bayyana cewa wannan ziyara na daga cikin muhimman matakai da kwamitin ke ɗauka wajen tattara bayanai na gaskiya, fahimtar yanayin aikin asibitoci, da gano abubuwan da ke kawo cikas wajen magance cutar tamowa a tsakanin yara.
Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai yi aiki tare da hukumomin lafiya, kungiyoyin agaji da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da ingantaccen tsari na ciyar da yara lafiya da kare lafiyarsu, musamman a yankunan karkara.
Husain Kabir Yar'adua