Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
A ci gaba da kiran Al'umma akan sabuwar Tafiyar Siyasar ADC a Nijeriya tsohon Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Sanata Abubakar Sadiq Yar'adua, ya gana da Abokan Siyasar sa na yankin Daura mai kananan hukumomi 12, don shiga cikin sabuwar jam'iyyar ADC.
Sanata Yar'adua da yake da Mukamin Babban Sakataren Tuntuɓa da karfafa Jama'a (Contect and Mobilisation) na ƙasa, ya shirya ganawar ne a jihar sa ta Katsina mai kananan hukumomi 34, inda ya ziyarci yankin Funtua a ranar juma'a, da yankin Katsina a ranar Asabar tare da tattaunawa da Wakilai daga yankin Daura a ranar Lahadi.
Sanatan ya jawo hankalin al'ummar jihar Katsina game da halin da kasa da kuma jihar take ciki game da Mulkin da ya kira na rashin imani da tausayin talakawa.
Sadiq yace "ko da yake babu bukatar wani dogon bayani dangane da halin da kasar take ciki, tunda abu ne wanda kowa ke ji a cikin jikin sa, amma dole in bayyana maku cewa, a matsayin ku na mutane na da muka yi tafiyar siyasa ta amana da ku, wasunsu tun daga shekarar 1998, zuwa yau, sai 'yan kadan. Kun Sanni kun san halina, kuma duk inda nake ko wace Jam'iyya ce bana goyon bayan rashin daidai. Don haka ku sheda nabar jam'iyyar APC da nayi takarar gwamna a cikin ta". Inji shi
Sanata ya bayyana cewa ya shiga jam'iyyar ADC Saboda ya fahimci ta dace da manufofin sa, da kuma abinda talakawa suke buƙata, don haka yanzu haka yana cikinta dumu-dumu tare da mukami babba daga matakin kasa baki daya.
Yace in tare daku kuma ina kira gareku da ku shiga jam'iyyar ADC ba tare da tilastawa ba, idan ma baku ra'ayin jam'iyyar ku sani zumuncin mu na nan.
Sanata yayi bayani dalla-dalla game da tsare-tsare da manufofin jam'iyyar ADC, daga ciki harda yadda za a bijiro da rijistar zama mamba ta hanya mai sauki, yace kuma na gode ma Allah wannan tsarin a karkashin ofishina yake, don haka jam'iyyar ADC ta kowa ce madamar nine a bangaren ba za a hada kai da ni a yi son zuciya ba.
Taron da ya gudana ranar Lahadi 17 ga watan Agusta 2025 a dakin taro na masaukin baki, Daura Motel ya samu halartar tsaffin masu ruwa da tsaki wakilan su daga kananan hukumomin Sanatan Shiyyar Daura.
An tattauna batutuwa da dama tare da nun sha'awar shiga sabuwar jam'iyyar daga mahalarta ciki hadda coordinator na kungiyar Gwagware Foundation na ƙaramar hukumar Bindawa Yahya Master dan jam'iyyar APC, da sauran yan siyasar yankin.