Matsalar tsaro a Najeriya batu ne na ‘Siyasa’ da aka bar wa Sojoji su magance shi — Buratai

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa  Tukur Buratai, ya bayyana cewa nasarar kawar da matsalar rashin tsaro a Najeriya tana buƙatar....

Katsina City News August 22, 2025  ·  12:00 AM
| 981 Views


Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa  Tukur Buratai, ya bayyana cewa nasarar kawar da matsalar rashin tsaro a Najeriya tana buƙatar cikakken tsari, yana mai jaddada cewa tushenta ya samo asali ne daga siyasa.

Buratai, wanda ya halarci shirin Sunrise Daily na tashar Channels Television, ya ce barin yaƙi da rashin tsaro a hannun sojoji kaɗai ba zai magance matsalar ba.

“‘Yan siyasa ne suka fara haifar da matsalar, kuma ainihin matsalar ta siyasa ce. Wannan rashin tsaro na da tushe a siyasa. Amma yanzu an bar wa sojoji ne kawai, sai kuma ‘yan siyasa suka koma gefe,” in ji tsohon hafsan sojojin wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

“Saboda haka akwai buƙatar a sake nazari gaba ɗaya kan harkar tsaro, musamman yadda siyasa da alakar ‘yan siyasa ke shiga cikin lamarin,” in ji shi.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 4?