@ Katsina Times
Jaridun katsina times sun tabbatar da dan ta addar nan na garin kankara ya saki matan garin mantau su 81 da ya kamo a harin da ya kai farkon satin nan.
Da misalin karfe goma na safiyar yau asabar wata majiya ta tabbatar ma da jaridun katsina times cewa Babaro ya sanya an dauko matan da ya dauka a garin mantau a kawo su kankara.
Majiyar jaridun katsina times tace Babaro yace sakin na jinkai da tausayawa ne babu wanda ya sashi.kuma in yaso ba karfin da zai iya kwatar su.
Majiyar katsina times tace Babaro ya roki matan su fadi gaskiya in sun koma gida cewa shi ya sako su ba tare da an bayar da ko anini ba ko kuma wata barazana ko karfi da akayi amfani dashi.
Matan sun iso garin kankara da misalin karfe sha biyu na rana.sojoji sun amshi matan inda yanzu suke shirin damka su ga karamar hukumar kankara zuwa kaisu garin Mantau.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Other social media handles. Katsina times
Jaridar taskar labarai
07043777779