Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Bashir Cheɗi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27082025_215607_IMG-20250827-WA0188.jpg

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana alhini kan rasuwar Malam Bashir Cheɗi, fnipr, memba a Majalisar Gudanarwa na Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR).

A saƙon ta’aziyyar da ya fitar ranar Talata, Ministan ya bayyana marigayin a matsayin babban rashi ga masu aikin hulɗa da jama’a a Nijeriya.

Ya ce: “Zuciya ta ta nauyaya da samun labarin rasuwar Malam Bashir Cheɗi, fnipr. Rasuwar sa ba wai rashi na musamman ga iyalin sa da abokan aikin sa na ƙwararru ba ne kawai, za ma a iya cewa babban ciwo ne ga dukkan masu aikin hulɗa da jama’a a Nijeriya.” 

Da Ministan yake bayani kan gudunmawar da Cheɗi ya bayar ta fiye da shekaru 30, ya tuna da rawar da ya taka a kamfanin Dornier Aviation Nigeria, da irin hidimar da ya yi wa ƙungiyar NIPR a matakin jiha da na ƙasa.

Ya ce, “Naɗin girmamawar da aka yi masa a matsayin Jagora (wato Fellow) na ƙungiyar ya cancanta ƙwarai; amma abin da ya fi, wannan shaida ce ta girmamawa da ƙaunar da ya samu ta hanyar tawali’u, hidima, da amana. Malam Cheɗi ya misalta mafi kyawun ɗabi’un masu aikin hulɗa da jama’a a Nijeriya.”

Idris ya ƙara da cewa za a tuna da Cheɗi saboda ƙwarewar sa wajen magance rikice-rikice, da hulɗa da hukumomi da kamfanoni, da taimakon al’umma, tare da tausayi da jajircewa wajen bada shawara ga matasa.

“A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ina miƙa ta'aziyya ga shugabanni da membobin Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya, da abokan aikin sa a Dornier Aviation Nigeria, da iyalin sa, da duk wanda ke jimamin wannan rashin da ba za a iya maye gurbin sa ba. Allah Maɗaukakin ya gafarta masa kurakuran sa, kuma ya ba shi hutu madauwami,” inji ministan.

Follow Us