Wasu matasa sun wargaza taron tsaro a katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02092025_141202_FB_IMG_1756822216102.jpg

@ katsina times 

Wasu matasa sun tarwatsa taron  katsina security community initiative da aka fara a dakin taro na Munaj, Matasan sun rika ihu da kiran kowa ya tashi sun yi kokarin fasa duk wata kyamera dake wajen.

Matasan sun rika jifa da kujerun da nuna dan ya tsa ga duk wanda suke ganin kamar makiyin wannan gwamnatin ne.

Mahalarta taron sunyi kokarin nuna jan wuya amma da aka lura wasu na boye da makamai a jikunan su aka ce kowa ya tashi gudun zubar da jini.

Masu taron yanzu haka sun shiga wani taron sirri a wani wajen sirri don daukar mataki na gaba.

Kyamarorin da akayi kokarin fasawa akwai na Arise TV da Trust tv Dana Katsina Times 
@ katsina times 
Www.katsinatimes.com

Follow Us