Tinubu Ya Umurci Karin Jami’an Tsaro a Katsina Bayan Taron Gaggawa da Tawagar Gwamna Radda a Aso Rock

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02092025_195422_FB_IMG_1756841592062.jpg


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara karfi da ƙaimi ga tsaron jihar Katsina, bayan wani muhimmin taro da ya gudanar da Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, tare da wata babbar tawaga daga jihar da suka nemi gaggawar shiga tsakani kan matsalar tsaro da ke ƙaruwa.

Shugaban ya umurci hukumomin tsaro su sake duba dabarunsu, tare da ƙara yawan jiragen sintirin sama (air drones), da kuma yiwuwar sake rarraba sojoji a Katsina da makwabtan jihohi don fuskantar barazanar ‘yan ta’adda kai tsaye.

“A yau na umurci hukumomin tsaro su ƙara kuzari, su sake nazarin dabarun da suke amfani da su. Za a ƙara tura jiragen sintiri na sama, kuma idan akwai buƙatar sake matsar da dakarunmu tsakanin Katsina da wasu iyakokin jihohi, za a yi hakan. Sun kuma ɗauki alƙawarin kawo rahoto a gobe,” in ji Tinubu.

Shugaban ƙasan ya amince da tsananin kalubalen tsaro da ake fuskanta a ƙasar, inda ya bayyana cewa:

“Matsalar tsaro da muke fuskanta ba ƙarama ba ce. Mun gada ne daga gazawa ta baya, musamman wajen kula da iyakokin ƙasa. Amma dole mu fuskance ta, kuma muna fuskantarta.”

Tinubu ya ƙara da cewa rundunar sojoji a ƙasa za ta tsananta aiki domin kawar da ‘yan ta’adda, yana mai jaddada:

 “Sojojin ƙasa suna nan, kuma za mu ci gaba da fatattakar su.”

Ya kuma bayyana shirin kafa ’yan sandan jihohi a matsayin wani muhimmin mataki na tsaro mai ɗorewa.

 “Dole mu kare ‘ya’yanmu, al’ummarmu, hanyoyinmu na rayuwa, wuraren ibada da nishaɗi. Ba za su tsoratar da mu ba.”

A jawabinsa, Gwamna Radda ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa bisa buɗaɗɗiyar ƙofar da yake da ita da kuma goyon baya mara yankewa ga jihar Katsina, inda ya ce duk buƙatun da aka gabatar masa ya kasance yana amincewa da su.

“Shugaban ƙasa ya nuna kansa a matsayin ɗan Katsina na gaskiya. Muna godiya bisa damuwarsa da matsalolin tsaro da ke damunmu,” in ji Radda.

A nasa bangaren, Sarkin Katsina wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, ya wakilta, ya roƙi Shugaban Ƙasa da ya ba da umarnin ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, tare da kafa bataliya ta soja da kuma sashen ‘yan sandan MOPOL a kudancin Katsina.

Ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta kashe sama da Naira biliyan 40 wajen tallafawa tsaro da kuma taimaka wa hukumomin tsaro na tarayya duk da ƙarancin kuɗin da ake da su, yana mai kira da a dawo da wani ɓangare daga gwamnatin tarayya da kuma tallafin taimakon waɗanda abin ya shafa.

Tawagar da ta raka Gwamna Radda sun haɗa da mataimakin gwamnan Katsina, Malam Faruq Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; tsohon gwamna Aminu Bello Masari; dukkan sanata uku na jihar; da ‘yan majalisar wakilai na tarayya daga Katsina.

Haka kuma akwai Ministan Ayyuka da Gidaje, ARC Ahmed Musa Dangiwa; Ministan Harkokin Fasaha da Al’adu, Barr. Hannatu Musa Musawa; Mai ba Shugaban Ƙasa shawara, Hajiya Hadiza Bala Usman; Jabiru Salisu Tsauri, shugaban AUDA-NEPAD Nigeria; da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.

Shugabannin gargajiya da addini da suka halarta sun haɗa da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar; Malam Yakubu Musa (Sautus Sunnah); tsohon mataimakin gwamnan Katsina, Alhaji Tukur Jikamshi; babban limamin Masallacin Juma’a na Katsina, Malam Gambo; da fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Wannan taro na zama wani sabon salo na dabarun kawo ƙarshen ta’addanci da ke addabar al’ummomin jihar Katsina da sauran yankin Arewa maso Yamma.

Follow Us