Jami'an tsaron Sibil Difens sun Kama Gidan Sauron Sata a Matazu, jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11092025_123718_FB_IMG_1757594084663.jpg



Daga Katsina Times

Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Katsina sun dakile yunƙurin karkatar gidan sauro da aka ware domin raba wa al’umma a ƙaramar hukumar Matazu.

Wata tawagar sintiri ta hukumar ta cafke wata motar Ford pickup mai lamba BDG 212 YE, ɗauke da buhuna 35, kowanne buhu na ɗauke da rigar gidan sauro 50, a lokacin da ake ƙoƙarin fitar da su daga Matazu zuwa Jihar Kano.

Bayan kamun, direban motar ya faɗa wa jami’an Sibil Difens cewa an ɗauke shi daga kasuwar Charanci domin ya ɗauko kaya daga Matazu zuwa Kano, ba tare da sanin nau’in kayan da aka loda masa ba. Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai wasu mutum huɗu da ake zargin suna da hannu a lamarin waɗanda suka tsere.

Kwamandan Sibil Difens na jihar, Ahmad, ya tabbatar wa jama’a cewa hukumar ba za ta yi sassauci ba wajen kare muradun al’umma da kuma tabbatar da an hukunta masu hannu a wannan aika-aika. Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da masu lalata kayayyakin gwamnati, masu cin amana da sauran miyagun laifuka da ke barazana ga jihar.

Kwamandan ya gode wa jama’a bisa goyon bayansu, tare da kira da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin kamo ɓarayi da masu tada fitina.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da jama'a ke ƙorafi cewa an raba gidan sauro amma da yawa wasu Unguwannin jihar Katsina Basu san ana yi ba, inda wasu ke zargin irin wannan almundahanar ta zagaye wasu jami'an da ke kula da rabon, har takai ya haddasa karancin rabon yadda ya kamata.

Follow Us