Karamar hukumar Matazu a jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar sulhu da Fulanin daji da suka dade suna addabar yankin, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga al’ummar yankin.
Sulhun ya gudana ne a ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025, a karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Hon. Shamsuddeen Muhammed Sayaya. An gudanar da taron a garin Dangeza, karamar hukumar Danmusa, tare da halartar manyan masu ruwa da tsaki da magadaddai na Matazu.
Kacallah Muhammadu, dan asalin Matazu wanda yake daya daga cikin shugabannin Fulanin daji, shi ne ya jagoranci bangaren Fulani wajen shiga yarjejeniyar. Ya bayyana cewa shi da mabiyansa sun amince da sulhun tare da yin alkawarin daina kai hare-hare da satar mutane a yankin, da kuma sako wadanda suke tsare a hannunsu.
A jawabinsa na maraba, Hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano, ya nuna farin cikinsa da samun wannan matsaya, inda ya bukaci al’umma da Fulanin daji su yafewa juna tare da zama cikin hadin kai da kwanciyar hankali.
Shugaban karamar hukumar, Hon. Shamsuddeen Sayaya, ya yi karin bayani kan muhimmancin wannan mataki, inda ya ce al’ummar Matazu sun yafe wa Fulanin daji duk abubuwan da suka faru a baya. Ya kuma nemi kafa kwamiti na hadin gwiwa tsakanin bangaren gwamnati da Fulanin daji domin samar da dandalin tattaunawa idan wani sabani ya taso a nan gaba.
Wasu daga cikin shugabannin Fulanin daji kamar Mannore da Alhaji Sani Yellow, sun yi korafe-korafe kan yadda jami’an tsaro ke takura musu, inda suka yi kira da a dauki matakan da za su tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Taron sulhun ya kasance wani sabon salo na kokarin kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi al’ummar Matazu da ma makwabtansu a jihar Katsina.