Katsina Times
Gwamnatin Tarayya tare da ta Jihar Katsina sun ƙara faɗaɗa shirin ɗaukar bayanai da koyar da sana’o’i ga matasa, inda tawagar sa ido daga gwamnatin jihar da ta tarayya ta shiga ƙananan hukumomi biyar a ranar Laraba, 24 ga Satumba 2025. Wannan mataki ya ɗaga adadin ƙananan hukumomin da shirin ya shafa zuwa 20 daga cikin 34 na jihar Katsina.
Sabbin ƙananan hukumomin da aka ziyarta sun haɗa da Kankia, Charanci, Dutsinma, Kusada da Ingawa. Shirin na gudana ne ƙarƙashin Hukumar Koyar da Ilimin Manya ta Ƙasa (NMEC) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Manya ta Katsina.
Shugabar hukumar a Katsina, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, ta bayyana cewa shirin ya fara ne da ƙananan hukumomi uku, amma daga baya aka yanke shawarar faɗaɗa shi zuwa 20 bayan nazarin bukatun jama’a a faɗin jihar.
Ta ce shirin ɗaukar bayanai da horar da matasa daga shekara 15 zuwa sama yana nufin samar musu da kayan aiki domin fara ƙananan sana’o’i, tare da tallafa musu wajen dogaro da kai.
Wannan ci gaban na nuna yadda gwamnati ke ƙara mai da hankali kan tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bunƙasa ƙananan masana’antu, rage rashin aikin yi, da kuma ba wa matasa damar samun sabbin hanyoyin rufin asiri.