China Ta Fara Taron Horas da Najeriya Kan Sabbin Fasahohin Kula da Jiragen Ƙasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22112025_193915_FB_IMG_1763840347080.jpg



KatsinaTimes | 22 Nov 2025

Gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wani babban taron horaswa na kasa da kasa kan tsarin sarrafa harkokin jiragen ƙasa ta hanyar fasahar zamani, wanda injiniyoyi da masana daga Najeriya ke halarta.

Taron, wanda aka fara a ranar 20 ga Nuwamba zai kare 4 ga Disamba 2025, yanzu haka taron na gudana ne a cibiyar China Railway Signal and Communication (CRSC) da ke Beijing, inda wakilai daga Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC), da Jami’ar Sufuri ta Daura (FUTD) ke halarta.

An shirya taron ne sakamakon yarjejeniyar hadin gwiwa da aka sanya a watan Agusta 2025 tsakanin Ma’aikatar Sufuri, Jami’ar FUTD da CRSC, wadda ta tanadi kafa cibiyar bincike ta hadin gwiwa kan fasahar kula da jiragen ƙasa da samar da kayan dakin gwaje-gwaje na zamani a Daura nan da shekarar 2026.

Yayin bude taron, Shugaban CRSC, Zhang Jingfang, ya ce halartar Najeriya babban ci gaba ne wajen fadada dangantakar fasaha a fannin sufurin jiragen ƙasa. Ya ce tun kafuwar CRSC a 1953, kamfanin ya jajirce wajen samar da tsare-tsaren kula da harkar jiragen kasa cikin tsaro da inganci a kasashen duniya.

Ya bayyana cewa fasahohin CRSC na aiki a kasashe sama da goma a nahiyoyi daban-daban ciki har da Najeriya, tare da yabawa gwamnatin Najeriya bisa amincewa da hadin gwiwa da kamfanin ke bayarwa.

A nata bangaren, Jakadiyar Najeriya a China, Amb. Ninikanwa Okey-Uche, ta gode wa CRSC bisa ci gaba da tallafa wa Najeriya, tare da tunatar da irin matakan da aka dauka tun ziyarar Ministan Sufuri na Najeriya zuwa CRSC a 2024 da kuma ziyarar da jami’an CRSC suka kai Najeriya a 2024.

Ta ce taron na da muhimmiyar rawa wajen inganta karfin kwararru a fannin kula da harkokin jiragen kasa da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin CRSC da Jami'ar FUTD domin gina cibiyar bincike ta Afrika a fannin fasahar sufuri.

Shugaban tawagar Najeriya, kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar FUTD, Farfesa Umar Adam Katsayal, ya jinjina wa Ma’aikatar Sufuri da CRSC bisa goyon bayan da suke bai wa jami’ar. Ya ce horon zai taimaka wajen kara ƙwarewa a sassan fasahar sigina, sadarwa, da sarrafa jiragen ƙasa tare da zurfafa hulɗar al’adu tsakanin ƙasashen biyu.

Follow Us