NWDC: Yankin Arewa maso yamma, ina muka dosa?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15122025_111346_IMG-20251215-WA0332.jpg



Yan makwanni da suka gabata, hukumar cigaban yankin kudu maso yamma (wato South West Development Commission SWDC), tare da hadin gwiwar hukumar jirgin kasa ta kasa wato NRC, sun rattaba hannu kan yarjejeniya domin hade dukkan jihohin yankin (Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti) da layin dogo na jirgin kasa. Za'a aiwatar da aikin ne da kudaden hukumar, da gudunmawar gwamnatocin jihohin yankin da kuma jarin kamfanoni masu zaman kansu. Ana shirya gabatar da shirin ga shugaban kasa domin amincewar sa, wanda ba shakka zai samu sahalewa cikin gaggawa.

Wannan cigaba, wanda zai iya sauya fasalin kudu maso yamma musamman ta fuskar sufuri idan aka aiwatar gaba daya, ya sa na waiwayo yankina na arewa maso yamma domin ganin abin da ta mu hukumar ta North West Development Commission NWDC ta cimma tun bayan kafuwarta a farkon wannan shekarar. Abin da na binciko ya tayar min da hankali matuka!

Daga cikin wadannan hukumomin cigaba guda shida na Najeriya, ta mu ta North West Development Commission ce ba ta da cikakken tsarin gudanarwa wato management team. Babban Darakta wato MD shi kadai aka nada. Babu Daraktocin gudanarwa, babu shugabannin sassa, babu ma’aikatan wucin gadi ko na dindindin da za su tafiyar da ayyukan yau da kullum. An nada kwamitin gudanarwa wato Board Members, amma kowa ya san aikinsu kulawa ne da sa ido. Ainihin aikin yana hannun hukumar gudanarwa, wanda har yanzu wata kusan goma, ba a kafa ba.

Matsala ta biyu, itace matsalar kudi wanda wannan babbar matsala ce. Kamar sauran sabbin hukumomin da aka kafa (South South, South West, South East da North Central), itama NWDC ba ta samu kudaden da doka ta tanadar mata ba. Wannan yasa ni zurfin tunani, shin mey ya sa gwamnati ke kafa sabbin hukumomi idan ta san ba za ta ba su kudin da za su tafiyar da aiki ba? Ta yaya ake tsammanin hukumar za ta cika aikinta ba tare da kayan aiki da kudaden gudanarwa ba?

Abin ya kara muni saboda akwai rikice-rikicen cikin gida tsakanin shugaban kwamitin gudanarwa wato Board Chairman da babban darakta wato MD. Ana samun tsoma baki daga shugaban kwamitin cikin ayyukan yau da kullum, wanda ainihin ya rataya ne a wuyan babban darakta. Har ma zabin ofishin wucin gadi na hukumar ya zama rikici. MD yana so a yi amfani da wurin da ke kan titin Murtala Muhammad Way a Kano saboda muhimmancinsa da tsaro, amma shugaban kwamiti shi kuma ya na jan kafa. Haka ma sauran muhimman takardu da suke bukatar sahalewa sun makale a teberin sa. Wannan rashin jituwa ta na ci gaba da kawo cikas tun kafin hukumar ta fara aikin ta gadan-gadan.

Duk da haka, NWDC ta riga ta tsara muhimman aiyuka da shawarwari a fannoni daban daban, kamar gine-ginen manyan aiyuka na more rayuwa, tsaro, noma, ilimi,  cigaban dan adam, lafiya da sauransu wadanda take shirin aiwatar da su a yankin.  Amma duk wadannan ba za su fara aiki ba muddin matsalolin da na zaiyana a sama ba a warware su ba.

Domin hukumar ta fara aiki yadda ya kamata, akwai bukatar daukar matakai cikin gaggawa. Dole gwamnatin taraiya ta kammala tsarin gudanarwa nan da nan, ta hanyar nada daraktoci da shugabannin sassa na hukumar. Sannan gwamnatin tarayya ya kamata ta saki kudin da doka ta ware domin hukumar ta samu kayan aiki, ta dauki ma’aikata, ta fara aiwatar da abubuwan da aka tsara. Haka kuma dole a girmama tsarin doka, shugaban kwamitin ya tsaya a bangaren sa na sa ido, yayin da babban darakta MD ke kula da harkokin yau da kullum.

Akwai bukatar a sasanta tsakanin shugabannin biyu domin daidaita al’amuran hukumar. Shiga tsakani daga gwamnoni da fitattun shugabannin arewa maso yamma zai iya kawo wa hukumar zaman lafiya da tsari. Haka itama hukumar ya kamata ta fitar da shirin aiki na guntun zango, da matsakaicin zango da kuma dogon zango domin jama’a su san da gaske suke.

Ya zama wajibi, Gwamnoni, wakilan majalisa, manyan shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki su shigo cikin lamarin hukumar nan da gaggawa, domin su warware matsalolin da suka shake wuyan hukumar. Yawancin sauran yankunan sun fara ganin amfanin hukumominsu. Arewa maso yamma bai kamata mu zamo a baya ba, dole mu yi wa tufkar hanci tun kafin bakin alkalami ya bushe!

An kafa wannan hukuma ne domin magance shekarun da yankin ya shafe ba tare da isasshen cigaba ba. Hukumar ba za ta fara wannan aiki ba muddin ba a nuna karfin siyasa da hadin kai daga shugabannin yankin ba, musammam wadanda abin ya shafa!

Da fatan sako na zai isa kunnan wanda abin ya shafa! 

Salihu Tanko Yakasai 
Dawisun Kanawa 
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya
14th December, 2025.

Follow Us