Hukumar Ilimin Manya ta Katsina Ta Yaye Mutum 200, Ta Ba Su Tallafin Jari
Daga Auwal Isah Musa
Katsina | Katsina Times
30 ga Disamba, 2025
Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina ta kammala shirin horas da sana’o’i na shekarar 2025, inda ta yaye maza da mata mutum 200 da aka zabo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar, tare da ba su tallafin jari domin dogaro da kai.
Shirin, wanda ya gudana tsawon makonni uku, na da nufin ƙarfafa ilimin manya da taimaka wa matasa da manyan da ba su samu damar karatun boko ba, ta hanyar koya musu sana’o’in hannu da dabarun kasuwanci.
An gudanar da bikin yaye daliban a ranar Talata a harabar Hedikwatar Hukumar Ilimin Manya da ke Kofar Durbi, Katsina. An fara rajistar shiga shirin ne tun a ranar 9 ga Disamba, inda aka fi bai wa matasa, mata da manya da ba su da damar samun ilimin boko muhimmanci.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina, Hajiya Bilkisu Mohammad Kaikai, ta bayyana shirin a matsayin wata babbar dama da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayar domin horas da iyaye, matasa maza da mata sama da shekaru 18, da sana’o’in dogaro da kai.
Ta ce mahalartan sun samu horo a sana’o’in da suka zaɓa, ciki har da kera takalma, haɗa turaren wuta da na fesawa, samar da kayan shafawa na mata, dinka rigunan mata da hijabai, kera zanen gado, hada sabulun ruwa da sauran sana’o’in samun kuɗin shiga.
Hajiya Bilkisu ta yaba da jajircewa da ƙwazon daliban tare da jinjinawa masu horaswa bisa rawar da suka taka wajen nasarar shirin. Ta kuma bayyana shirin hukumar na faɗaɗa wannan shiri zuwa dukkan shiyyoyin jihar.
Shi ma Shugaban masu horaswa kuma mai ba da shawara ga shirin, Dr. Chucks Okehie, ya yabawa Gwamna Dikko Umar Radda bisa ƙoƙarinsa na bunƙasa rayuwar al’ummar jihar, yana mai bayyana shirin a matsayin abin koyi. Ya ce kusan kashi 80 cikin 100 na mahalarta matasa ne, inda wasu daga cikinsu suka fara amfani da kuɗin sufuri wajen sayen kayan aiki tun kafin kammala shirin.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin ginshiƙin ci gaba.
“Ba za a samu ci gaban al’umma ba sai da ilimi da samar da ayyukan yi. Wannan shiri ya haɗa duka biyun,” in ji gwamnan.
Gwamna Radda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gina mutane da bunƙasa tattalin arzikin jihar, tare da alƙawarin faɗaɗa shirin zuwa dukkan ƙananan hukumomi. Ya kuma shawarci daliban da su yi aiki da gaskiya da inganci a sana’o’in da suka koya.
A ƙarshe, an bai wa kowane ɗalibi shaidar kammala horo, tallafin kuɗi na Naira dubu 30, da katin shiga rukunin aiki na musamman (VISA). Haka kuma, an yi wa wasu fitattun dalibai rajista da Hukumar CAC, an ba su lambar haraji (TIN), tare da haɗa su da Hukumar KASEDA domin samun rancen kuɗi marar ruwa da sauran damarmaki.
Taron ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da Sarkin Kurayen Katsina, Alhaji Usman Darda’u Kuraye; Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar; manyan jami’an gwamnati, wakilan SUBEB da KASEDA, da sauran al’umma.