Daga Muazu Hassan | Katsina Times.
Kungiyar dattawan Arewa reshen jahar katsina ( ACF) ta yi zargin mataimakin shugaban Kungiyar na kasa Sanata Ibrahim Idah wazirin katsina da neman yi mata karfa karfa da kokarin hana su aikinsu da kin yarda da wadanda "yan kungiyar suka zaba a matsayin shugabannin su a jahar katsina.
Wannan korafi na a cikin wata takarda da zababben shugaban kungiyar Alhaji Shehu Musa Malumfashi ( wazirin galadiman katsina) ya rubuta ga membobin kungiyar mai taken halin da kungiyar ACF reshen jahar katsina ke a ciki.
A cikin takardar shugaban kungiyar ya kawo bayanin kafuwar kungiyar da yadda suka yi zabe kamar yadda tsarin mulkin kungiyar ya tanada.
A takardar sunyi bayanin hatta nasarorin da suka samu harda samarwa kungiyar ofis a ginin gidauniyar jahar katsina wanda mai martaba sarkin katsina ya bada.
A takardar sunyi korafin cewa mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Sanata Ibrahim Idah wazirin katsina yana ta basu matsala na kin yarda da shugabancinsu da bita da kulli kala kala.
A takardar sunyi korafin cewa Ana kokarin gabatar da wasu a matsayin sune shugabannin kungiyar alhali su basu a cikin masu biyan kungiyar kudaden da aka tsara na shekara shekara.
Jaridun katsina times sunyi kokarin jin ta bakin Sanata Idah abin ya ci tura..sun aika masa sakon rubutu na waya ba amsa.sun kira shi bai dauki waya ba.
Jaridun katsina times sun samu labarin shugabannin ACF na zasu kawo ziyara ga gwamnan katsina a yau alhamis. Amma an kange shugabannin jaha sanin me ake ciki.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page/group. Katsina city News
Jaridar Taskar labarai..
All social media handles. @ katsina times
07043777779