Daga Mu’azu Hassan
@ Katsina Times
Sabuwar jam’iyyar nan ta ADC wadda ke ta samun tagomashi a duk faɗin ƙasar nan, kuma take zama yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Nijeriya.
Jam’iyyar ta zama matattarar sabbi da tsofaffin ’yan siyasa waɗanda ba su da ra’ayin shiga ko ci gaba da zama cikin jam’iyyar APC saboda mabambantan ra’ayoyi.
A Katsina, jam’iyyar ta yi nasarar jawo wasu fitattun ’yan siyasa a cikinta. Kusan kowace shiyyar ɗan Majalisar Tarayya da ta Sanata ka ɗauka, akwai wani fitacce a cikinta.
A shiyyar Funtua, jam’iyyar ta yi nasarar samun ’yan siyasa irin su tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Malumfashi/Ƙafur, wanda aka fi sani da Babbangida Talau, da irin su Janar Maharazu Tsiga.
A shiryar Katsina akwai irinsu Sanata Saddiq Yar’adua da Dakta Mustapha Muhammad Inuwa.
A shiyyar Daura akwai irin su Sanata Ahmed Babba Kaita da sauran su, waɗanda dukkansu ’yan siyasa ne da tarihi ya san su da tasirinsu a zaɓe da kuma cin zaɓe.
A Katsina, babbar matsalar jam’iyyar ADC ita ce shigowar Alhaji Lawal Daura a cikinta, da kuma yadda ya shigo da shelar cewa zai yi takarar Gwamnan Katsina.
Kila da shigowa ya yi da sunan ɗan jam’iyya, yana sha’awar koyon siyasa, har malamanta su tabbatar cewa ya cancanta ya tsaya takara irin wadda zai iya taimakon jiha da ƙasa, su ba shi takarar dai bayan sun gwada tunani da ƙwarewarsa a wannan fagen ba tare da matsala ba.
Siyasa makaranta ce mai zaman kanta, wadda duk wanda yake son a tsayar da shi ko ya tsaya takara, sai ya zo cikin ajinta ya koya a aikace, ba karatun Aku ko na Malam Bambadiya ba.
Tarihi da misalai masu dama sun tabbatar mafi yawan masu shiga siyasa daga shigarsu su faɗa neman takara ba su taɓa kai bentensu ba.
Wasu idan suka ɗau lokaci suka koyi siyasa, suka kuma yi biyayya, ana yarda da su a ba su takara, kuma su yi nasara. Misali, marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Malam Nuhu Ribadu ma da takara ya fara siyasa, har yanzu bai ci zaɓe ba.
Kwarewarka a sanin siyasar bincike kamar wani malamin Jami’a, ko sanin siyasa ta bayanan sirri na tsaron ƙasa, ko na ɗauko rahoto irin na jarida, ba shi ne tabbacin ka san siyasa ba.
Ko da ka san waɗancan, idan ka shigo ta, sai ka sad da kai ka koyi ta a aikace, sannan a nuna maka hanyar nasara.
Tarihi da misalai birjik sun nuna duk wanda ya bar wani wurin ƙwarewarsa ya faɗa siyasar takara, ba yakan yi nasara ba.
Misali, a zaɓen da ya gabata a jihar Bauchi, tsohon Janar na soja wanda ya kai ƙololuwa (Air Marshal), duk da ƙarfin Gwamnatin Tarayya, ya kasa cin zaɓe a jihar. Gwamnan jihar ya kayar da shi kaye mai kyau, wanda har Gwamnatin Tarayya ta rasa inda za ta dogara ta soke zaɓen.
Abin da Lawal Daura ya kamata ya yi wa kansa karatu ne na natsuwa ya sani shi ne; babu wani ɗan siyasa da zai yarda ya miƙa kansa a zaɓe shi a matsayin Gwamna a zaɓen 2027.
Gwamna fa! Wani aro ne da Allah ke ba bawansa daga ƙarfin mulkinsa. Shin ke nan ɗan siyasa daga shigowarka jiya, kuma daga gidan tsaro, sai ya sallama maka kansa na tsawon shekaru huɗu?
Ɗan siyasa ya san kansa, ya kuma fi yarda da ɗan uwansa ɗan siyasa; ba wanda ya yi wankan tsarki ba. Idan har ta kama a nemo wanda za a tsayar takara, ɗan siyasa idan zai ɗauko wani ba a cikinsu ba, sai an lale, an duba, an tantance sannan a samu matsaya. Matsayar ba irin su Lawal Daura ake ɗaukowa ba.
Kwanan nan, Gwamnan Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa ya je garin Daura domin amsa gayyatar wani babban ɗan Lawal Daura da ya yi wani tallafi ga matasa. Ka fahimta, babban ɗan Lawal Daura na cikinsa. Ya gayyaci Gwamnan Katsina wajen ba da tallafin da ya shirya, kuma har Gwamnan ya ba gidauniyar gudunmawar kuɗi don faɗaɗa aikinta.
Ina ganin wannan na nufin “something is wrong somewhere”. An fara koya wa Lawal Daura wani sabon karatu a siyasa. Wannan wani saƙo ne wanda idan ya ci gaba zai iya zama wani “integrity tsumani”.
Abin da Lawal Daura ya kamata ya yi shi ne ya ajiye gurinsa na takara. Ɗan siyasa ya iya ƙunar baƙin wake a neman mulki. Idan ka dage, ya juya maka baya, ya sa a fasa kowa ya rasa.
Misalin abin da ya faru a zaɓen 2015 inda wasu gwamnonin PDP suka juya mata baya daga rikicin zaɓen shugaban gwamnoni, wanda ya jawo faɗuwarta.
Haka kuma a 2023 da Wike suka yi wa Atiku Abubakar shaƙar ƙamshin mutuwa kan rikicin zaɓen mataimaki, yana cikin dalilan faɗuwar Atiku.
Ni na yi imani har ga Allah da wasu gogaggun ’yan siyasar nan, su bar Lawal Daura ya zama Gwamna gara a fasa kowa ya rasa, kuma za su yi hakan ne a ƙurarren lokaci.
Lawal Daura ya ajiye gurinsa na zama Gwamna a gefe. Ya yi biyayya ga malaman siyasar da ke ADC. Ya fara ɗaukar karatu tun daga ƙolo yadda ƙwaƙwalwarsa ke ja, zuwa zaɓe na gaba sai su yi nazarinsa su ga wace takara za su ba shi.
Wannan shawara ce kyauta Fisabilillahi.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Facebook page. Jaridar Taskar labarai
All social media handles. Katsina times
0704377779.08057777762