’Yan Sandan Jihohi: Wani Dodo Ne Da Wata Rana Zai Zama Abin Tsoro a Ƙasar Nan

Daga Danjuma KatsinaHalin da harkokin tsaro suka shiga a ƙasar nan ba za a warware shi kawai ta hanyar ƙirƙirar ’yan sandan jihohi ba. A ganina, ƙirƙirar ’yan sandan jihohi…

Katsina City News August 12, 2026  ·  12:00 AM
| 80 Views
’Yan Sandan Jihohi: Wani Dodo Ne Da Wata Rana Zai Zama Abin Tsoro a Ƙasar Nan
’Yan Sandan Jihohi: Wani Dodo Ne Da Wata Rana Zai Zama Abin Tsoro a Ƙasar Nan


Daga Danjuma Katsina

Halin da harkokin tsaro suka shiga a ƙasar nan ba za a warware shi kawai ta hanyar ƙirƙirar ’yan sandan jihohi ba. A ganina, ƙirƙirar ’yan sandan jihohi na iya ƙara dagula al’amura maimakon ta taimaka, domin akwai yiyuwar ya zama wata ajanda da wasu ’yan siyasa ko wasu ɓangarorin ƙasar nan ke nema, wadda wata rana za ta iya zama kamar wani dodo da zai tsoratar da al’umma.

Idan da gaske ake son magance matsalar tsaron ƙasar nan, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata a fara dubawa.

Na farko, tun a zamanin mulkin Janar Ibrahim Babangida, an yi hasashen cewa wata rana yawan jama’a da faɗaɗar ƙasar za su ƙaru, kuma matsalolin tsaro za su iya ƙaruwa. Saboda haka aka fara tunanin yadda za a shirya ƙasa tun kafin matsalolin su yi tsanani.

A cikin ’yan sanda, an inganta wata runduna da aka dade da kafawa, wato Mobile Police (MOPOL). An rika ba jami’anta horo mai kama da na soja, ciki har da horon aiki a daji, tare da samar musu da ingantattun makamai. A wancan lokaci, ana girmama rundunar MOPOL a matsayin wata babbar rundunar yaƙi da matsalolin tsaro.

Ina MOPOL suke a yau? Me ya sa aka rage musu irin wannan horo da ƙarfin aiki? Da an ci gaba da inganta su, da suna iya taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.

Na biyu, an taɓa ƙirƙirar wata runduna da ake kira Quick Intervention Force, wadda ta yi aiki na wasu shekaru. Ayyukanta sun haɗa da kai ɗaukin gaggawa yayin rikice-rikicen cikin gari. An ba jami’anta horo kan yadda za su kare kansu da kuma yadda za su shawo kan rikici.

Da an ci gaba da inganta wannan sashe na ’yan sanda, da yana iya taimakawa sosai wajen magance matsalolin daba, fashi, kwacen waya da sauran laifukan da ke faruwa a cikin birane.

Haka kuma akwai SARS, wadda aka rusa a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari. Babban aikin wannan sashe shi ne yaƙi da fashi da makami. Da an gyara matsalolin da suka shafi wannan runduna tare da inganta tsarin aikinta, da ita ma za ta iya taka muhimmiyar rawa.

Waɗannan sassa uku suna da amfani sosai idan aka gyara su, aka samar musu da ƙwararrun jami’ai, aka inganta albashinsu, aka ba su horo mai inganci, kayan aiki na zamani da kuma dokokin aiki masu kyau. Za su iya taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar tsaron garuruwanmu.

Na biyu, gwamnatoci daban-daban sun kafa kwamitoci domin duba yadda za a tsara da inganta aikin ’yan sanda. Ɗaya daga cikin na ƙarshe shi ne wanda marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya kafa ƙarƙashin jagorancin marigayi M. D. Yusuf. A cikin kwamitin akwai tsoffin shugabannin ’yan sanda na ƙasa guda biyar, waɗanda suka gudanar da aiki suka kuma gabatar da rahoto.

Ina wannan rahoton yake? Me ya ƙunsa? Ina rahotannin sauran kwamitocin da aka kafa a baya? Me suka ba da shawara? Me ya sa ba a aiwatar da su ba?

An kafa waɗannan kwamitoci tun kafin matsalar tsaro ta kai ga inda take a yau. Misali, an miƙa rahoton ƙarshe a shekarar 2010. Na karanta rahoton, kuma na ga abubuwan da aka rubuta a cikinsa.

Tabbas, da wata gwamnati ta aiwatar da shawarwarin da rahoton ya bayar, da ba mu kai wannan matsayi da muke ciki yanzu ba.

Rahoton ya bayyana yadda za a gyara aikin ’yan sanda ya zama ingantaccen aikin ƙasa, tun daga gyaran ɗabi’a da tarbiyya, horo, albashi, kayan aiki da kuma jin daɗin jami’ai.

Rahoton ya kuma bayyana yadda wasu masu aikata laifuka ke iya ɗaukar nauyin wasu mutane domin su shiga aikin ’yan sanda, don su samu mutanen da za su yi musu aiki daga cikin hukumar. Rahoton ya nuna hanyoyin da za a bi domin dakile irin wannan matsala.

Na uku, a zamanin mulkin Babangida, an taɓa ƙoƙarin kafa wata runduna mai suna National Guard. An tattaro jami’ai daga sassa daban-daban na hukumomin tsaro, aka kai su sansanin horo a dajin Sambisa, inda aka fara ba su horo na musamman.

Tsarin da aka tsara shi ne idan wata matsalar tsaro ta taso wadda ta fi ƙarfin Quick Intervention Force ko MOPOL, to a tura National Guard kafin matsalar ta zama babbar barazana ga ƙasa.

Sai dai aka dakatar da wannan shiri kafin ya kai ga cikakken nasara. Da an ci gaba da shi, akwai yiyuwar ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaron ƙasar nan.

Advertisement

NRS Gateway

Na huɗu, kwamitoci daban-daban sun bayar da shawarwari kan yadda za a inganta aikin sojojin Najeriya. Ɗaya daga cikin na baya-bayan nan an kafa shi a lokacin gwamnatin Buhari.

Tambaya ita ce: Nawa daga cikin shawarwarin waɗannan kwamitoci aka aiwatar?

Shawarwarin sun shafi komai, tun daga ɗaukar sojoji zuwa horo da kayan aiki. Me aka yi da rahotannin da ake gabatar wa gwamnatin tarayya?

Sojoji suna yawan korafin cewa har ma da kuɗaɗen da aka ware musu a kasafin kuɗi ba sa samun su a kan lokaci. Idan bukatar gaggawa ta taso, sai an rubuta buƙata, an kai ta ga shugaban ƙasa, sannan a jira amincewa. Kafin a fitar da kuɗin, matsalar na iya ƙara girma fiye da abin da aka fara neman kuɗin domin magancewa.kullum kudin da ake ba sojojin suna yin biyan bashin daddawar kauye ne..

Bangaren DSS ma ya sha fama da matsalolin kuɗi, horo da kayan aiki. Sai a ƙarƙashin shugaban hukumar na yanzu aka samu wasu sauye-sauye da suka inganta aikinta. Amma har yanzu akwai sauran abin da ya kamata a yi.

A ganina, gyara da inganta hukumomin tsaronmu bisa shawarwarin da suke gabatarwa ga gwamnatin tarayya shi ne babban abin da zai taimaka wajen inganta tsaro a ƙasar nan. Haka kuma ya kamata a duba yiwuwar farfaɗo da wasu hukumomin tsaro ko sassan tsaro da aka rage wa ƙarfi ko aka rusa, kamar MOPOL, Quick Intervention da National Guard.

’Yan Sandan Jihohi

Duk muhawarar da ake yi kan ’yan sandan jihohi, za ka fi jin muryoyin ’yan siyasa da waɗanda ke goyon bayan wannan tsarin, musamman daga wasu ɓangarorin kudancin ƙasar nan. Amma ina masana harkokin tsaro na gaskiya? Me ya sa yawancinsu suke yin shiru?

Gaskiyar magana ita ce, rudanin da ke cikin wannan kuduri ya fi amfanin da ake tsammanin zai kawo yawa.

Misali, a Katsina, shin za a  jira ’yan sandan jiha ne su warware mana matsalar tsaro? Yaushe za a ɗauke su? Yaushe za a ba su horo? Yaushe za a ba su kayan aiki? Yaushe za su fara aiki? Shin su ne za su rika shiga daji suna fafatawa da ’yan bindiga?

Gwamnatin Katsina ta kafa Jami’an Tsaron Al’umma, kuma gaskiya sun taka rawa wajen gano masu bai wa ’yan bindiga bayanai. Sun kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen gano maboyar ’yan bindiga da kuma kai hare-hare a kansu.

Idan aka kafa ’yan sandan jiha, shin za a rusa waɗannan jami’an ne? Ko kuwa ’yan sandan jiha ne za su maye gurbinsu?

Jihohi suna ta kokawa kan ƙarancin kuɗaɗen shiga da kuma nauyin ayyukan da ke kansu. To, ta yaya za su ɗauki nauyin wata babbar hukuma mai kama da ’yan sandan jiha? Shin za a rika ba kowace jiha kuɗi daga gwamnatin tarayya ne? Ko kuwa za a bar kowace jiha ta nemi kuɗin kanta?

Jami’in tsaro wanda yake cikin matsanancin buƙata, rayuwarsa ta lalace, kuma tarbiyyarsa ta lalace, na iya zama hatsari fiye da barawon daji.

Abin da nake tsoro shi ne, idan aka kafa ’yan sandan jihohi, wata rana za mu rika jin labarin cewa an ɗauko wani ɗan Arewa a wani yanki na Kudu, an kai shi ofishin ’yan sandan jiha, an tuhume shi, sannan aka kai shi kotu—kamar yadda ake ganin wasu jami’an tsaro na sa-kai a wasu jihohi a yanzu.

A Arewa kuma, akwai yiyuwar ’yan sandan jihohi su zama makami a hannun masu mulki ko masu kuɗi. Wata rana za su iya zama dodanni waɗanda za su fara farautar duk wanda ya yi musu adawa ko wanda ba ya goyon bayan waɗanda suka taimaka wajen kafa su

Saboda haka, kafin a yi gaggawar kafa ’yan sandan jihohi, ya kamata a fara gyara da ƙarfafa hukumomin tsaron da suke nan, a aiwatar da shawarwarin kwamitocin da suka yi nazari kan matsalolin tsaro, sannan a dawo da wasu tsare-tsaren tsaro da suka kasance suna da amfani.

Domin matsalar tsaron Najeriya ba ta rasa hukumomin tsaro ba; abin da ta fi rasa shi ne ingantaccen tsari, kayan aiki, horo, kuɗaɗen aiki, shugabanci nagari da kuma cikakken aiwatar da shawarwarin da masana suka gabatar.

Danjuma shine mawallafin jaridun katsina times da katsina city news magazine 

Ana iya samunsa a 08020570059

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 4?