Auwal Isah Musa | Katsina Times
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ta bayyana shirin raba gidajen sauro masu magani da kuma rigakafin cutar cizon sauro ga yara ‘yan watanni 3 zuwa 59, a wani gagarumin gangami da za a gudanar a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Shirin ya fito fili ne yayin wani taron manema labarai da ma’aikatar ta gudanar a ranar Talata, inda aka yi karin bayani kan yadda za a gudanar da aikin da kuma irin matakan da za a dauka don tabbatar da nasararsa.
Jami’in Shirin Lafiyar Iyali ta Kasa (NHCP), Gbue Denen Daniel, ya bayyana cewa za a raba gidajen sauro masu dauke da maganin kashe sauro (ITNs) sama da miliyan 4 a fadin jihar, tare da rigakafin cutar cizon sauro (SPAQ) fiye da miliyan 9 ga yara ‘yan watanni 3 zuwa 59.
Ya bayyana cewa an tanadi wuraren rabon gidajen sauro a unguwanni daban-daban, inda wadanda aka riga aka yi wa rajista za su je da kati domin karɓar kayayyakin. A bangaren rigakafin yara kuwa, za a rika zagaya gida-gida ana bayar da maganin, bayan an kammala rajistar da ake gudanarwa a halin yanzu.
“Mutum da bai da kati, ba zai samu kayan rigakafin ba,” in ji Daniel, yana mai cewa bayanan da aka tattara a lokacin rajistar za su taimaka wajen sanin adadin gidajen sauro da za a bai wa kowanne gida, ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa wadda za ta tantance mutanen da suka cancanta.
A cewarsa, rigakafin yara zai shafi ne kawai wadanda suke cikin shekarun da aka kayyade (watanni 3-59) kuma wadanda ba su da zazzabin cizon sauro a lokacin bayarwar, domin “maganin na rigakafi ne, ba na warkarwa ba.”
Ya kara da cewa shan maganin zai kasance ne a gaban jami’in lafiya, sannan kuma a ci gaba da shan sa na tsawon kwanaki uku a jere domin samun cikakkiyar kariya. Haka kuma, an bukaci iyaye su tabbatar da cewa ‘ya’yansu na kwanciya a cikin gidajen sauro don kare su daga kamuwa da cutar.
Daniel ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na yunkurin gwamnati wajen kawar da cutar cizon sauro a jihar, tare da hadin gwiwar Shirin Kawar da Maleriya na Kasa (NMEP), da kuma tallafin Global Fund Malaria Project.
A yayin taron, shi da takwararsa Catherine Igoh sun haska wani faifan bidiyo da ke nuna irin illar cutar maleriya ga al’umma, musamman a lokacin damina, da kuma matakan kariya da suka hada da amfani da gidajen sauro da shan rigakafin cutar.
Ma’aikatar ta bukaci hadin gwiwar kafafen yada labarai da sauran ‘yan kasa wajen yada wannan muhimmin sako domin ceton rayukan al’umma, musamman kananan yara.