Dalilin Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina a Abuja

Mu’azu Hassan @Katsina TimesTsawon kwanaki ana ta yada jita-jitar cewa an tsare Babban Dogarin Gwamnan Katsina (ADC) da kuma Babban Jami’in Tsaron Gwamnan (CSO) a hedkwatar ’yan sanda da kuma…

Katsina City News August 25, 2026  ·  12:00 AM
| 140 Views
Dalilin Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina a Abuja
Dalilin Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina a Abuja

Mu’azu Hassan @Katsina Times

Tsawon kwanaki ana ta yada jita-jitar cewa an tsare Babban Dogarin Gwamnan Katsina (ADC) da kuma Babban Jami’in Tsaron Gwamnan (CSO) a hedkwatar ’yan sanda da kuma ta Hukumar DSS da ke Abuja.


Binciken da Katsina Times ta gudanar ya gano cewa, lallai, jami’an tsaron biyu suna hannun jami’an tsaro a Abuja.


Binciken ya kuma tabbatar da cewa har Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Nasir, ya je Abuja domin kokarin ganin an sako jami’an, amma abin ya ci tura.


Wata majiya ta ce hatta Gwamnan Katsina ya yi kokarin ganin an sako jami’an da aka dora wa alhakin kare lafiyarsa, amma har zuwa yanzu lamarin bai yiwu ba.


To, me ya faru?

Akwai wasu manyan allunan tallace-tallace da ke kan hanyar shatale-talen Modoji zuwa Gidan Gwamnatin Katsina. Wadannan alluna na dauke da sakonni daban-daban na siyasa, da hotunan Gwamnan Katsina, Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa da kuma wasu ’yan siyasa.

Binciken Katsina Times ya gano cewa an wayi gari an lalata wasu daga cikin wadannan manyan alluna, ciki har da wasu da ke dauke da hotunan Shugaban Kasa da kuma mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Masari.

Advertisement

NRS Gateway


Bisa wannan lamari na lalata allunan, musamman wadanda ke dauke da hotunan Shugaban Kasa, an rubuta korafi zuwa ga Rundunar ’Yan Sanda da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).


Binciken Katsina Times ya kuma gano cewa jami’an tsaro sun kama wani mutum da ake zargi da kasancewa shugaban wata kungiyar siyasa ta bangar siyasa a Katsina, mai suna Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Aminu Nasta.


Bayan kama shi, ana zargin cewa bisa bayanan da ya bayar ne aka gayyaci wadannan jami’an tsaron Gwamnan Katsina domin yi musu tambayoyi.


Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, jami’an biyu suna tsare a Abuja, bisa zargin cewa suna da masaniya kan lamarin ko kuma sun taimaka wajen kare wadanda ake zargi da lalata allunan da ke dauke da hotunan Shugaban Kasa.


Sai dai tambayar da ke ci gaba da kasancewa ita ce: Mene ne hakikanin abin da ya faru, kuma wane irin alaka ce ke tsakanin jami’an tsaron Gwamnan da lamarin lalata wadannan alluna?

Binciken jaridun katsina times ya gano wasu hirarraki da akeyi a shafukan Facebook yana kara dagula lamarin ne fiye da gyara halin da ake ciki.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 5?