Cutar Mashaƙo: Ƙananan Hukumomi 29 suna cikin Barazana A Katsina" Hukumar Lafiya

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)Gwamnatin Jihar Katsina ta ce an samu waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashaƙo a ƙananan hukumomi 29 na jihar.Mukaddashiyar Babbar Sakatariyar Hukumar Kula…

Katsina City News August 30, 2026  ·  12:00 AM
| 34 Views
Cutar Mashaƙo: Ƙananan Hukumomi 29 suna cikin Barazana A Katsina"  Hukumar Lafiya
Cutar Mashaƙo: Ƙananan Hukumomi 29 suna cikin Barazana A Katsina" Hukumar Lafiya


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)


Gwamnatin Jihar Katsina ta ce an samu waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashaƙo a ƙananan hukumomi 29 na jihar.


Mukaddashiyar Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta jihar (KSPHCA), Dakta Shaima’u Kabir Abba, ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi, 30 ga Agusta, 2026, yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a hedikwatar hukumar da ke Katsina.


Ta ce duk da cewa an samu waɗanda ake zargin sun kamu da mashaƙo a ƙananan hukumomi 29, ƙananan hukumomi 24 ne suka fi fuskantar matsalar, yayin da sauran wuraren da aka samu masu cutar suka haɗa da Kankia, Katsina, Mai’adua da Daura.


Dakta Shaima’u ta bayyana halin da ake ciki a matsayin abin damuwa, amma ta tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin jihar na ɗaukar matakan da suka dace domin dakile yaɗuwar cutar.


Ta ce mashaƙo cuta ce mai hatsari amma ana iya kare kai daga gare ta ta hanyar rigakafi, kuma tana iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da yawan allurar rigakafi bai kai matakin da ake buƙata ba.


A cewarta, Ƙungiyar Shirye-shiryen Gaggawa da Martanin Gaggawa ta jihar, tare da Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko, Ma’aikatar Lafiya, Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), NCDC da sauran kungiyoyin lafiya, sun ƙara kaimi wajen dakile yaɗuwar cutar.


Ta ce ana gudanar da sa ido kan cutar, gano mutanen da suka yi hulɗa da waɗanda ake zargin sun kamu da ita, tattara bayanan waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar, nazarin bayanai da kuma ba wa waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar magungunan kariya.


Dakta Shaima’u ta ce gwamnatin jihar ta fara wani shirin rigakafin gaggawa a ranar 25 ga Agusta a ƙananan hukumomi biyar da aka gano cewa su ne suka fi fuskantar barazanar mashaƙo.


Ta ce ana gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar NPHCDA, yayin da UNICEF ke bayar da tallafin kayan aiki da sauran abubuwan da ake buƙata.


Ta bayyana cewa zuwa rana ta uku na aikin, mutane 67,670 da suka cancanci rigakafin sun karɓi allurar Td, yayin da yara 24,103 suka karɓi allurar pentavalent a ƙananan hukumomin biyar da ake gudanar da shirin.


Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samu ƙarin allurai 650,000 na rigakafin mashaƙo, domin faɗaɗa aikin rigakafin da kuma kare al’ummomin da cutar ta fi kamari.


Mukaddashiyar Babbar Sakatariyar ta ce gwamnatin jihar ta kafa ƙarin cibiyoyin masu dauke da cutar guda uku domin inganta kula da waɗanda suka kamu ko ake zargin sun kamu da mashaƙo.


Ta ce cibiyoyin sun haɗa da MCHC Kankia Babban Asibitin Funtua da General Amadi Rimi Orthopaedic dake Katsina.

Advertisement

NRS Gateway


Ta ce gwamnati na kuma samar da magunguna, kayan aikin jinya da kayan kariya daga yaɗuwar cututtuka domin tallafa wa cibiyar masu masu dauke da cutar ta NCDC da ke Federal Teaching Hospital Katsina.


A cewarta, an kuma tanadi magungunan kula da masu cutar a wuraren da mashaƙo ta fi kamari, yayin da ake ƙara horas da ma’aikatan lafiya kan sa ido da kuma kula da masu cutar.


Dakta Shaima’u ta ce gwamnati ta ƙara kaimi wajen neman waɗanda ake zargin sun kamu da mashaƙo, gano mutanen da suka yi hulɗa da su, sa ido kan yaɗuwar cutar da kuma ba da magungunan kariya ga waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar.


Ta ce ana kuma ƙarfafa matakan kariya daga yaɗuwar cututtuka a cibiyoyin lafiya, tare da raba kayan kariya ga ƙananan hukumomin da abin ya shafa.


Ta ce daga cikin ƙalubalen da ke gaban aikin dakile mashaƙo akwai rashin samun isasshen adadin mutane da ke karɓar rigakafi, jinkirin kai waɗanda ake zargin sun kamu da cutar asibiti, da kuma iyakar ƙasa mai sauƙin ketarewa tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.


Ta ce gwamnati na aiki tare da abokan hulɗarta domin shawo kan waɗannan matsaloli, tare da ƙarfafa shirin rigakafin yau da kullum domin rage yawan yaran da ke cikin haɗarin kamuwa da cututtukan da ake iya kare kai daga gare su ta hanyar rigakafi.


Dakta Shaima’u ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun karɓi dukkan alluran rigakafin


Ta kuma buƙaci jama’a da su gaggauta zuwa asibiti idan su ko ’ya’yansu suka fara nuna alamun mashaƙo, ciki har da ciwon makogaro, zazzabi, wahalar haɗiye abinci ko numfashi, kumburin wuya, ko kuma wani farin ko toka mai kauri da ke bayyana a makogaro, ko hanci.


Ta ce bai kamata a jira sai yanayin mara lafiya ya tsananta ba, ko kuma a yi ƙoƙarin magance wanda ake zargin ya kamu da mashaƙo a gida.


“Gaggauta kai mara lafiya cibiyar lafiya na iya ceton rai, sannan ya taimaka wajen hana yaɗuwar cutar ga ’yan uwa da sauran al’umma,” in ji ta.


Ta kuma yi kira ga al’ummomi da su ba ƙungiyoyin masu aikin rigakafi, jami’an sa ido da sauran ma’aikatan lafiya haɗin kai yayin da suke gudanar da ayyukansu a wuraren da cutar ta shafa.


Dakta Shaima’u ta yaba wa Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, NPHCDA, NCDC, UNICEF, WHO da sauran abokan hulɗar bisa tallafin da suke bai wa jihar wajen tunkarar annobar.


Ta kuma yaba wa sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, hukumomin ƙananan hukumomi, masu wayar da kan jama’a, ma’aikatan lafiya, jami’an sa ido da ƙungiyoyin rigakafi bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare al’umma.


Ta tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin Gwamna Dikko Umar Radda za ta ci gaba da samar da abubuwan da ake buƙata domin shawo kan mashaƙo, ƙarfafa sa ido da kula da masu cutar, da kuma inganta tsarin rigakafin yau da kullum domin kare yara daga cututtukan da ake iya hana su ta hanyar rigakafi.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 3?