SAUKA DAGA KUJERAR GWAMNATIN KATSINA! SAI KUMA WA? – NAZARI

Daga Katsina TimesA wannan makon ne Mai Bai wa Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan Harkokin Raya Al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye mukaminsa.Katsina Times ta gano cewa Alhaji Tsanni ya…

Katsina City News September 24, 2026  ·  12:00 AM
| 52 Views
SAUKA DAGA KUJERAR GWAMNATIN KATSINA! SAI KUMA WA? – NAZARI
SAUKA DAGA KUJERAR GWAMNATIN KATSINA! SAI KUMA WA? – NAZARI


Daga Katsina Times


A wannan makon ne Mai Bai wa Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan Harkokin Raya Al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye mukaminsa.

Katsina Times ta gano cewa Alhaji Tsanni ya mika takardar ajiye mukaminsa ga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, inda ya bayyana godiyarsa bisa damar da aka ba shi ta yi wa gwamnati hidima.


Da yake zantawa da Katsina Times, Alhaji Tsanni ya bayyana cewa a yanzu ya samu cikakkiyar dama, wato kashi 100 cikin 100, domin mayar da hankali kan aikin kungiyoyin da yake jagoranta, musamman shirye-shiryen sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Dikko, da kuma sauran ’yan takarar jam’iyyar APC.


Hadiza Yar’Adua ita ma ta bar kujerar?


Kafin Alhaji Abubakar Tsanni, an samu irin wannan lamari da ya shafi Hadiza Yar’Adua, wadda a baya ta rike mukamin Kwamishiniya, kafin daga bisani aka sauya mata matsayi zuwa Mai Bai wa Gwamnan Katsina Shawara.


Sai dai sama da watanni yanzu an daina jin duriyarta a bainar jama’a, lamarin da ya haifar da rade-radi daban-daban.


Wasu na cewa Hadiza Yar’Adua ta ajiye mukaminta, yayin da wasu ke cewa tana hutun aiki ne.


Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Katsina Times ba ta samu cikakken bayani a hukumance kan matsayin ta ba.


Advertisement

NRS Gateway

Suleiman Namadi Shama ma ya ajiye mukami

A ranar 22 ga watan Satumba, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Zaizayar Kasa da Koguna ta Jihar Katsina (Katsina State Erosion and Watershed Management Agency), Alhaji Suleiman Namadi Shama, shi ma ya ajiye mukaminsa.


Binciken Katsina Times ya gano cewa akwai wasu masu rike da mukaman gwamnati da ke da irin wannan niyya, sai dai dalilan da ke tattare da matakin nasu sun bambanta.

Wasu daga cikinsu na da kusanci da wasu manyan ’yan siyasar APC da ke Abuja, ko kuma suna da kusanci da wasu masu fada-a-ji a jam’iyyar a matakin tarayya.


Wasu kuma na ganin cewa, duk da kasancewarsu cikin gwamnati, ba a ba su damar taka rawar da suke ganin ya dace su taka ba.


saboda haka, ake ganin wasu daga cikinsu na duba yiwuwar sauya alkiblar siyasarsu ko matsayinsu a cikin APC.


Menene burinsu?


Binciken Katsina Times ya nuna cewa, duk da bambancin dalilan da ke sa wasu daga cikin masu rike da mukaman gwamnati tunanin ajiye mukamansu, akwai wata manufa guda da ta hada wasu daga cikinsu: su mayar da hankali wajen ganin jam’iyyar APC ta samu nasara.

Wasu daga cikinsu kuma na fatan cewa, idan aka samu nasarar siyasa, za a iya ba su wasu mukamai a matakin tarayya a Abuja, maimakon ci gaba da rike mukamai a Katsina.


Yanzu dai abin jira shi ne ganin ko a cikin kwanaki masu zuwa za a sake samun wasu masu rike da mukaman gwamnati da za su ajiye mukamansu.


Sai kuma wa? Lokaci ne zai  bayyana.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 9?