Hon. Abdulkadir Zakka na shirin ficewa daga jam iyyar APC

Rahoton Musamman@ Katsina TimesMajiyoyi daban-daban daga ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina sun tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa tsohon ɗan siyasa mai riƙe da muƙamai daban-daban, Hon. Abdulkadir…

Katsina City News October 19, 2026  ·  12:00 AM
| 61 Views
Hon. Abdulkadir Zakka na shirin ficewa daga jam iyyar  APC
Hon. Abdulkadir Zakka na shirin ficewa daga jam iyyar APC


Rahoton Musamman

@ Katsina Times

Majiyoyi daban-daban daga ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina sun tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa tsohon ɗan siyasa mai riƙe da muƙamai daban-daban, Hon. Abdulkadir Zakka, na shirin ficewa daga jam’iyyar APC.

Zakka ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Safana na tsawon shekaru takwas. Haka kuma, ya taɓa zama kantoman ƙaramar hukumar Safana, tare da kasancewa zababben shugaban ƙaramar hukumar a wani lokaci.

Baya ga haka, ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Katsina, sannan ya yi aiki a matsayin mai ba Gwamnan Katsina shawara kan ayyuka na musamman. A shekarar 2023, ya kuma tsaya takarar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Hon. Abdulkadir Zakka ya shafe tsawon lokaci yana harkokin siyasa, inda ya fara tun a shekarar 1978. Ya fara ne da ƙungiyar P.U, daga baya ya koma PRP, sannan PF, kafin ya shiga jam’iyyar SDP, inda ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Tsare-Tsare na jam’iyyar a matakin jiha.

Zakka yana da tasiri da karfi a cin zabe a  karamar hukumar safana 

A wani sabon al’amari, majiyoyi daban-daban sun shaida wa Katsina Times cewa Zakka na tattaunawa da Alhaji Yakubu Lado, ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, da kuma Ahmad Babba Kaita, wanda ake dangantawa da takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Sai dai, a lokacin da Katsina Times ta tuntubi Hon. Abdulkadir Zakka domin jin ta bakinsa kan rahotannin da ke cewa yana shirin ficewa daga APC, ya bayyana cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar, amma yana tattaunawa da mutanensa kafin ya yanke matsaya ta ƙarshe.

Advertisement

NRS Gateway

A cewarsa:

“Na shafe shekaru 48 ina harkokin siyasa, kuma na riƙe muƙamai daban-daban. Ina da jama’a, don haka muna tattaunawa da su kafin mu yanke hukunci,” in ji Zakka yayin tattaunawarsa da Katsina Times.

Wannan bayani na Zakka ya nuna cewa, duk da cewa har yanzu yana cikin APC, yana ci gaba da tattaunawa da mutanensa kafin yanke shawarar matakin siyasa na gaba.

Katsina times 

Facebook page: katsina city news

Facebook group. Katsina city News 

Facebook page.jaridar Taskar labarai 

Website: www.katsinatimes.com 

07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 6?