SHIRIN BUNKASA RAYUWAR AL’UMMA (CDP) YA ZIYARCI ƘANANAN HUKUMOMI BIYU DOMIN DUBA AYYUKAN CI GABA

A ci gaba da ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina na bunƙasa rayuwar al’umma tun daga tushe, Shirin Bunƙasa Rayuwar Al’umma (CDP) ya kai ziyarar sa ido zuwa ƙananan hukumomi biyu domin…

Katsina City News November 19, 2026  ·  12:00 AM
| 113 Views
SHIRIN BUNKASA RAYUWAR AL’UMMA (CDP) YA ZIYARCI ƘANANAN HUKUMOMI BIYU DOMIN DUBA AYYUKAN CI GABA
SHIRIN BUNKASA RAYUWAR AL’UMMA (CDP) YA ZIYARCI ƘANANAN HUKUMOMI BIYU DOMIN DUBA AYYUKAN CI GABA


A ci gaba da ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina na bunƙasa rayuwar al’umma tun daga tushe, Shirin Bunƙasa Rayuwar Al’umma (CDP) ya kai ziyarar sa ido zuwa ƙananan hukumomi biyu domin duba ayyukan raya ƙasa da aka gudanar a matakin mazabu.


Tawagar shirin ta gudanar da wannan ziyara ne a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Jami’in Hulɗa da Jama’a na shirin, Alhaji Ashiru Mamman Ingawa, wanda ya wakilci Shugaban Shirin, Associate Professor Kamaluddeen Kabir.


Ƙananan hukumomin da tawagar ta ziyarta sun haɗa da Funtua da Bakori.


A Ƙaramar Hukumar Funtua, an ziyarci mazabun Sabon Gari, Dan-Dutse, Unguwar Ibrahim, Unguwar Musa da Unguwar Rabi'u (Mace).


A Ƙaramar Hukumar Bakori kuma, an ziyarci mazabun Kwaremi (Mace), Bakori A, Bakori da Kabomo.

Advertisement

NRS Gateway


Ayyukan da aka gudanar a ƙarƙashin shirin sun haɗa da gyaran makarantu, gyaran rijiyoyi da ƙananan asibitoci, gina sabbin gine-gine, gyaran masallatai, samar da ruwan sha, da sauran ayyukan da ke da nufin inganta rayuwar al’umma.


A yayin ziyarar, Alhaji Ashiru Mamman Ingawa ya bayyana irin gagarumin ci gaban da Shirin CDP ke kawowa a matakin mazabu a faɗin Jihar Katsina. Ya duba ayyukan da aka gudanar tare da bayyana gamsuwarsa da ci gaban da aka samu, sannan ya ba da shawarwari kan wuraren da ake buƙatar ƙarin gyara domin tabbatar da inganci.


Tawagar ta kuma samu damar zagayawa kai tsaye zuwa wuraren da ake gudanar da ayyukan, ciki har da waɗanda ba a kammala ba, domin tantance yanayin aikace-aikacen da kuma tabbatar da ingancin ayyukan.


Shirin Bunƙasa Rayuwar Al’umma (CDP) na daga cikin manyan ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na bunƙasa rayuwar al’umma da samar da ayyukan ci gaba a faɗin jihar.


A nasu ɓangaren, al’ummomin da suka amfana da ayyukan sun bayyana jin daɗinsu da godiyarsu bisa irin ayyukan ci gaban da aka samar musu, tare da nuna goyon bayansu ga shugabancin jam’iyyar APC.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 8?