KO TSARIN “RAINBOW COALITION” NA MINISTAN ABUJA, WIKE, ZAI SHAFI GWAMNAN KATSINA DA SAURAN ’YAN TAKARA?

Binciken Jaridun Katsina TimesKwanan nan, wasu gwamnonin sukayi wani  korafi kan wani shiri da ake zargin an yi tsakanin Ministan Abuja da wani ɓangare na jam’iyyarsa ta PDP. Da wasu…

Katsina City News October 12, 2026  ·  12:00 AM
| 117 Views
KO TSARIN “RAINBOW COALITION” NA MINISTAN ABUJA, WIKE, ZAI SHAFI GWAMNAN KATSINA DA SAURAN ’YAN TAKARA?
KO TSARIN “RAINBOW COALITION” NA MINISTAN ABUJA, WIKE, ZAI SHAFI GWAMNAN KATSINA DA SAURAN ’YAN TAKARA?

Binciken Jaridun Katsina Times

Kwanan nan, wasu gwamnonin sukayi wani  korafi kan wani shiri da ake zargin an yi tsakanin Ministan Abuja da wani ɓangare na jam’iyyarsa ta PDP. Da wasu jiga-jigan gwamnatin tarayya da na APC 

Ana kiran wannan shiri da Turanci da suna “Rainbow Coalition”. 

kwanan nan ma, wani ɗan majalisar tarayya daga Jihar Kano mai suna Jibrin ya fito ya kare tsarin, inda ya bayyana cewa ba zai cutar da zaɓen shugaban ƙasa ba.

Wani sanata mai suna Ashemole ya bayyana wa manema labarai cewa Wike yana yi wa shugaban ƙasa aiki ne, ba wai yana yi wa jam’iyyar APC aiki ba.

Kalamai daban-daban da aka yi ba tare da an fito an karyata su ba sun ƙara tabbatar da zargin cewa akwai wannan tsari.

Ana zargin cewa manufar tsarin ita ce Ministan Abuja, Wike, ya tabbatar da raunana jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa.

Ana kuma zargin cewa tsarin ya ba Wike damar gina mutanensa a cikin PDP, sannan a kyale su su shiga zaɓe a matakai daban-daban, tun daga na gwamna zuwa na ’yan majalisun tarayya da na jihohi.

A yadda ake zargin tsarin zai gudana, akwai wasu jihohin da za a kyale masu zaɓe su zaɓi ’yan takarar da suke so a matakin ’yan majalisun tarayya, wanda za a fara da shi. Amma a zaɓen shugaban ƙasa, za a tabbatar da cewa an zaɓi Tinubu.

Haka kuma, a zaɓen gwamnoni, za a kyale zaɓe ya gudana cikin kwanciyar hankali, ba tare da tsoma baki ba, ciki har da zaɓen ’yan majalisun jihohi.

A zurfin binciken da Katsina Times ta gudanar, ta tabbatar da cewa ana zargin wannan tsari yana wanzuwa a matakin sirri tsakanin wasu manyan ’yan siyasa.

“Ka san sirrin siyasa ba a kan takarda ake yin sa ba. A’a, magana ce ta ɗaukar alƙawari da kyakkyawar fahimtar juna. Tinubu kuma ya ƙware a wannan fanni, kuma bai taɓa saɓa alƙawarin da aka yi da shi ba,” in ji wani mutum da ya yi iƙirarin sanin sirrin tsarin, yayin da yake magana da babban editan jaridun Katsina Times ido da ido.

KO TSARIN ZAI SHAFI JIHAR KATSINA?

A dai-dai lokacin da muka kammala wannan rahoto, majiyoyi daban-daban a gwamnatin tarayya da jam’iyyun APC da PDP sun tabbatar mana da cewa, idan ba a samu sauyi ba, Jihar Katsina tana cikin wannan tsari.

Advertisement

NRS Gateway

Ma’ana, ana zargin cewa Jihar Katsina na daga cikin jihohin da aka miƙa wa Wike a ƙarƙashin shirin sirri na “Rainbow Coalition”.

“Ni na yi aiki a kan Katsina. Mun tsara yadda shugaban ƙasa zai ci Katsina da gagarumin rinjaye, da kuma ’yan majalisun tarayya da za a taimaka wa. Daga nan, za a kyale zaɓe ya yi halinsa,” in ji wani mutum da ya yi magana da babban editan jaridun Katsina Times ido da ido.

“Na zauna da mutane uku a wani katafaren masaukin baki. Fuskokinsu na nuna natsuwa da kwarin gwiwar samun nasarar abin da suke shiryawa, kuma suna karɓar umarni. Mun shafe sa’o’i uku muna tattaunawa, sannan muka ɗauki wasu sa’o’i huɗu muna cin abinci,” in ji babban editan Katsina Times.

Idan bayanan da muka samu gaskiya ne, zaɓen 2027 zai gudana yadda ya kamata, ba tare da katsalandan ko tagomashin gwamnatin tarayya ba.

“Haka muke son a yi zaɓe, ba tare da katsalandan ba. APC na yin kurakuran siyasa da za mu yi amfani da su. Aikin ci gaba daban yake, kuskuren lissafin siyasa da cin zaɓe kuma daban yake. Muna da makamai masu linzami; lokacin sakin su kawai muke jira,” in ji wani jigo a jam’iyyar adawa.

KO APC A KATSINA TA SAN DA WANNAN TSARIN MAI WUYA?

Bincikenmu ya nuna cewa ana zargin wasu jiga-jigan APC a Katsina sun san da wannan batu. Hatta gwamnan ya taɓa bayyana cewa ana yi masa ƙulle-ƙulle a Abuja.

Haka kuma, gwamnan ya sha nanata cewa Allah ne ke ba da mulki a jawabansa. Ya kan ce: “Ko mun dawo ko ba mu dawo ba.”

Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa irin waɗannan kalamai na iya zama saƙon ishara da ke nuna cewa gwamnan yana sane da abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa.


Facebook page..katsina city News 

Facebook group..katsina city News 

Facebook page..jaridar taskar labarai 

@ www.katsinatimes.com. 07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 1?