Siyasar Rashin Bayyana Hoton Tinubu a Katsina

Daga Abubakar AbdullahiKatsina, Mazaunin kadunaDa farko, a iya cewa wannan ba wani sabon labari ba ne da ya kamata ya ɗauki hankali sosai. Jam’iyyun siyasa suna sauya salo da zane-zanen…

Katsina City News October 09, 2026  ·  12:00 AM
| 98 Views
Siyasar Rashin Bayyana Hoton Tinubu a Katsina
Siyasar Rashin Bayyana Hoton Tinubu a Katsina


Daga Abubakar Abdullahi

Katsina, Mazaunin kaduna


Da farko, a iya cewa wannan ba wani sabon labari ba ne da ya kamata ya ɗauki hankali sosai. Jam’iyyun siyasa suna sauya salo da zane-zanen kayayyakinsu, ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe kuma suna da ’yancin tsara abubuwansu yadda suka ga dama. Ba lallai ba ne kowace fasta ko kowace motar siyasa ta kasance da hotunan dukkan shugabannin siyasa.


Tsawon shekaru da dama, ’yan siyasa suna amfani da hotuna wajen isar da saƙonnin alaƙa, biyayya da kusanci da masu madafun iko. Idan ɗan takara ya sanya hoton Shugaban Ƙasa tare da na Gwamna da nasa hoton, yana son masu zaɓe su gan shi a matsayin wani ɓangare na tsarin siyasa da ya faro daga Abuja, ya ratsa babban birnin jiha, har ya kai ga mazabarsa.


 Saboda haka, idan hoton da aka saba gani a kusan ko’ina ya fara ɓacewa daga wasu kayan siyasa, a dabi’ance mutane za su fara tambayar dalili.


Kwanan nan, Babban Sakataren Gwamna Dikko Umaru Radda na musamman, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, ya raba motoci guda 10 a Ƙaramar Hukumar Rimi domin gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da ƙarfafa goyon bayan siyasa. An yi wa motocin tambarin wannan shiri na siyasa na cikin gida, amma abin lura shi ne, hoton Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai bayyana a jikinsu ba. 


An kuma lura da irin wannan yanayi a wasu motocin da Gwagware Foundation ta raba. Wannan gidauniya wata muhimmiyar cibiyar goyon bayan siyasa ce da ake dangantawa da Gwamna Radda. 


Duk da cewa gidauniyar tana da alaƙa mai ƙarfi da Gwamnan da kuma tafiyar siyasarsa, an lura cewa wasu daga cikin motocin da aka yi wa tambari a baya-bayan nan ba su ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa ba.


Haka kuma, ana ta tattaunawa kan kayayyakin yaƙin neman zaɓe da ke da alaƙa da Abba Dahiru Mangal, ɗan takarar APC na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Katsina Central. Wasu daga cikin fastocinsa da ake yaɗawa a bainar jama’a sun fi jaddada takararsa da kuma kasancewarsa ɗan APC, ba tare da nuna hoton Shugaba Tinubu ba. Duk da haka, babu wani daga cikin waɗannan misalai da zai iya tabbatar da cewa akwai saɓanin siyasa da Shugaban Ƙasa. Amma idan irin waɗannan abubuwa suka faru sau da dama a cikin yanayin siyasa guda, to hakan yana haifar da wata babbar tambaya.


Ya kamata a lura cewa babu wani daga cikin waɗannan abubuwa, ko an duba su ɗaiɗaiku ko a haɗe, da ya isa ya zama hujjar cewa Gwamna Radda, magoya bayansa ko ’yan takarar da abin ya shafa sun juya wa Shugaba Tinubu baya. Yin irin wannan hukunci zai zama gaggawa. Amma wannan salo yana haifar da tambayar siyasa mai ma’ana: Shin akwai wani sauyi a yadda ake bayyana biyayya ta siyasa a cikin APC ta Katsina? Wannan tambaya ta cancanci kulawa, musamman yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaɓen shekarar 2027.


A Najeriya, fastocin zaɓe sun wuce matsayin kayan talla kawai, domin su ma wani harshe ne na siyasa. Idan ɗan takara ya sanya hotonsa tare da na Shugaban Ƙasa da Gwamna, yana gaya wa masu zaɓe cewa yana cikin gida ɗaya na siyasa da waɗannan shugabanni. Dalili kuwa shi ne, hoton Shugaban Ƙasa yana nuna alaƙa da matakin ƙasa; hoton Gwamna yana nuna kusanci da goyon baya a matakin jiha; yayin da hoton ɗan takara yake bayyana wanda ke neman amincewar masu zaɓe. 


Idan aka haɗa hotunan ukun, suna samar da wani tsari na jagorancin siyasa da ido ke iya fahimta:


 Shugaban Ƙasa, Gwamna da ɗan takara.

Ga talaka mai zaɓe, wannan saƙo na iya zama mafi sauƙin fahimta fiye da dogon jawabin siyasa. Ka yi tunanin wani manomi a Rimi da ya ga motar yaƙin neman zaɓe tana ratsa cikin al’ummarsa. 


Wataƙila bai san cikakken bayani game da tattaunawar siyasa da ake yi a Abuja ko Katsina ba. Wataƙila bai taɓa halartar taron shugabannin APC ba. Amma ya san Shugaba Tinubu, ya san Gwamna Radda, kuma ya san ɗan takarar. 


Hotunan ukun suna gaya masa cewa waɗannan mutane suna tare. Wannan shi ne dalilin da ya sa tambarin siyasa yake da muhimmanci. Yana ƙarfafa fahimtar cewa jam’iyyar tana aiki a matsayin ƙungiya guda, ba tarin ƙungiyoyin siyasa masu fafatawa da juna ba.


Tsawon wani lokaci, tsarin siyasar da aka saba gani a Katsina ya kasance mai sauƙin fahimta: Tinubu, Radda da ɗan takara. Wannan tsari ya kasance yana da amfani ta fuskar siyasa da kuma tunanin masu zaɓe. 


Ga ɗan takara, alaƙa da Shugaban Ƙasa da Gwamna na iya ƙara masa karɓuwa da amincewa a idon jama’a. Ga Gwamna, kasancewar hoton Shugaban Ƙasa yana ƙarfafa alaƙarsa da jagorancin jam’iyyar na ƙasa. Ga Shugaban Ƙasa, bayyanar hotonsa a kamfen na jiha yana nuna cewa tsarin siyasar yankin yana da alaƙa da babban burinsa na ƙasa. Ga mai zaɓe kuwa, saƙon yana ba shi kwarin gwiwa cewa mutanen da suke neman ƙuri’arsa suna gabatar da kansu a matsayin ƙungiya guda.


Wannan yana da muhimmanci musamman a Jihar Katsina, inda alaƙar siyasa da hanyoyin sadarwar mutum-da-mutum suke ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tattara goyon bayan masu zaɓe. Saboda haka, hoton ya zama wani ɓangare na muhimman kayan aikin siyasa.


A irin wannan yanayi ne rashin hoton Tinubu a wasu motocin siyasa da fastoci na baya-bayan nan ya jawo tattaunawa. Misali, an yi motocin Rimi ne domin tallafa wa ayyukan wayar da kan jama’a da tattara goyon bayan siyasa a matakin ƙasa-ƙasa, waɗanda ke da alaƙa da tsarin siyasar Gwamna. 


Ƙungiyar kamfen ta cikin gida na iya yanke shawarar fifita shugabannin siyasar da suke kusa da ita maimakon manyan shugabannin ƙasa. Haka nan za a iya yin irin wannan bayani game da faston ɗan takara. Wataƙila ɗan takara ya ga cewa sunansa, hotonsa da tambarin jam’iyyarsa sun isa.


Amma ba wai manufar wanda ya tsara saƙon siyasa ce kaɗai ake la’akari da ita ba. Ana kuma la’akari da yadda masu kallo suka fahimci saƙon. Magoyin bayan APC da ya saba ganin Tinubu da Radda tare zai iya lura da lokacin da Tinubu ya ɓace daga hoton. Zai iya tambaya: Me ya sa? Wani kuma zai iya tambaya: Shin akwai saɓani tsakanin Katsina da Abuja? Wani na ukun kuwa zai iya ɗauka cewa ɗan takarar ya fi kusanci da Gwamna fiye da Shugaban Ƙasa. Wataƙila wannan fahimta ba ta dace da gaskiya ba, amma a siyasa, fahimtar jama’a ba koyaushe take jiran samun hujja ba.


Advertisement

NRS Gateway

Akwai wani muhimmin al’amari da bai kamata a manta da shi ba a wannan tattaunawa: Gwamna Radda ya sha bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu a bainar jama’a. Masu ruwa da tsaki na APC a Katsina sun nuna goyon bayansu ga Tinubu domin takarar Shugaban Ƙasa ta shekarar 2027, yayin da Gwamna Radda ya sha kira ga ’yan jam’iyyar da su ƙara himma wajen tattara goyon baya ga Shugaban Ƙasa. Haka kuma, Gwamnan ya sha danganta ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da ci gaba da manufofi da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa. 


Saboda haka, akwai manyan alamu da ke nuna cewa alaƙar siyasa ta hukuma tsakanin Tinubu da Radda tana nan daram.


Tambayar ba lallai ba ce ko Radda yana goyon bayan Tinubu. Tambayar da ta fi jan hankali ita ce ko wasu daga cikin ɓangarorin tsarin siyasar da ke kewaye da Gwamnan suna fara gina wata siyasa da ta fi karkata ga Radda da kansa, maimakon haɗin gwiwar Tinubu da Radda.


 Wannan bambanci yana da muhimmanci. Tsarin siyasa na iya ci gaba da kasancewa mai biyayya ga Shugaban Ƙasa, a lokaci guda kuma yana ƙara mayar da hankali kan harkokin siyasar jiha. Amma idan wannan karkata ga siyasar jiha ta yi ƙarfi fiye da kima, a ƙarshe za ta iya haifar da tunanin cewa akwai rarrabuwar kai da jam’iyyar na ƙasa.


Wannan tattaunawa ba za ta rasa kawo batun dangantakar da aka daɗe ana magana a kai tsakanin Gwamna Radda da Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Ba Shugaba Tinubu Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa da Sauransu. Mutanen biyu ba baƙi ba ne a siyasar Katsina. Hanyoyin siyasarsu sun daɗe suna haɗuwa, kuma tsarin siyasar da ke da alaƙa da tsohon Gwamna Aminu Bello Masari ya taka muhimmiyar rawa wajen fitowar Radda a matsayin babban ɗan siyasa. 


Sai dai abubuwan da suka faru a fagen siyasa a baya-bayan nan sun haifar da hasashen cewa akwai muradu daban-daban da ke kewaye da Gwamnan da kuma wasu manyan ’yan siyasa masu tasiri a Abuja.


Rahotanni da tattaunawar siyasa game da dangantakar sun bambanta. Wasu na nuni da yiwuwar samun saɓanin siyasa, yayin da wasu ke cewa abokan hamayyar siyasa ne suke ƙara girman waɗannan bambance-bambance. 


A siyasa, abin da jama’a suka yi imanin yana faruwa na iya zama da tasiri kamar abin da yake faruwa a zahiri. Idan ’yan APC suka fara yarda cewa akwai cibiyoyin iko guda biyu masu fafatawa da juna; ɗaya a kusa da Gwamna a Katsina, ɗaya kuma a kusa da manyan ’yan siyasa masu tasiri a Abuja, jam’iyyar na iya fara samun rarrabuwar biyayya a hankali.


Rashin hoton ba shi ne ainihin matsalar ba. Matsalar gaske ita ce abin da hoton zai iya fara wakilta. A kowace jam’iyyar siyasa akwai muradu daban-daban, kuma hakan abu ne na al’ada. ’Yan siyasa masu burin samun matsayi za su fafata wajen neman tikitin takara, tasiri, muƙamai da karɓuwa. Jam’iyya mai ƙarfi tana sarrafa waɗannan buri daban-daban a cikin tsari guda, yayin da jam’iyya mai rauni take barin su su rikide zuwa ƙungiyoyin ɓangaranci.


Idan wata ƙungiya ta fara kasancewa sananniya a matsayin ta Gwamna kawai, wata kuma ta zama ta ’yan siyasa masu tasiri a Abuja, yayin da wasu suka karkata ga ɗaiɗaikun ’yan takara ko masu ɗaukar nauyin siyasa masu kuɗi, APC na iya tsintar kanta da injinan siyasa daban-daban da ke aiki ƙarƙashin sunan jam’iyya guda.


Hakika, irin wannan yanayi zai haifar da sakamako. Zai iya rikitar da ’yan jam’iyya a matakin ƙasa-ƙasa, ya raunana haɗin gwiwar tattara goyon baya, ya sa takarar tikitin jam’iyya ta ƙara rikitarwa, ya zurfafa rashin yarda tsakanin masu riƙe da mukaman siyasa, sannan ya bai wa jam’iyyun adawa damar samun sauƙin abin da za su yi amfani da shi wajen yaƙin neman zaɓe. Ba lallai ne ’yan adawa su tabbatar da cewa shugabannin APC suna faɗa da juna ba. Za su iya kawai nuna ƙungiyoyin siyasa daban-daban su ce jam’iyyar ba ta ƙara zama tsintsiya madaurinki ɗaya ba.


Shugaba Tinubu yana da muhimmiyar muradin siyasa a Katsina. Jihar ba wani yanki ne na zaɓe kawai ba. Tana daga cikin muhimman jihohin siyasa a Arewacin Najeriya, tana da dimbin masu zaɓe (it ace ta hudu a kasar nan) da kuma tsarin jam’iyya mai tushe mai zurfi. 


Idan APC tana son samun gagarumin goyon baya ga Tinubu a Katsina a zaɓen 2027, Shugaban Ƙasa yana buƙatar ƙungiyar jam’iyya mai ƙarfi da haɗin kai a jihar. Wannan kuma yana buƙatar haɗin gwiwa da Gwamna Radda.


Haka nan, Gwamna Radda yana buƙatar kyakkyawar dangantaka da jagorancin APC na ƙasa da kuma Gwamnatin Tarayya. Saboda haka, ya kamata dangantakar siyasar ta kasance mai ƙarfafa juna. 


Amma duk wani abu da zai haifar da tunanin cewa waɗannan muradu suna fafatawa da juna maimakon su taimaki juna, ya kamata ya jawo hankalin shugabannin jam’iyyar.


Idan APC a Katsina tana da niyyar tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya samu gagarumin goyon baya a zaɓe, ya kamata matsayin Shugaban Ƙasa a tsarin siyasar jam’iyyar ya ci gaba da kasancewa a bayyane a cikin shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe. 


Wannan ba yana nufin cewa dole ne kowace mota ko kowace fasta ta ɗauki hotonsa ba. Yaƙin neman zaɓe yana buƙatar sassauci, kuma akwai dalilai masu inganci da za su sa a tsara wasu kayan kamfen ta wata hanya dabam.


Amma a tsarin manyan dabarun siyasa, ci gaba da nuna alaƙar jagorancin ƙasa da na jiha na iya ƙarfafa fahimtar cewa jam’iyyar tana da haɗin kai. Idan hoton Tinubu ya ci gaba da ɓacewa daga kayan kamfen na wasu ƙungiyoyin APC, yayin da hoton Radda yake nan a fili, masu lura da siyasa na iya fara fassara hakan a matsayin alamar cewa cibiyar ƙarfin siyasar tana sauyawa daga Abuja zuwa Katsina. 


Ko wannan fahimta ta dace da gaskiya ko a’a, ya kamata jam’iyyar ta san cewa irin wannan fahimta na iya yaɗuwa.


Saboda haka, ba zai dace ba a ayyana cewa rashin hoton Shugaba Tinubu a jikin motocin Rimi, motocin Gwagware Foundation ko wasu fastocin kamfen na Abba Dahiru Mangal yana tabbatar da rashin biyayya ta siyasa. 


Amma idan wannan ya zama wani ɓangare na babban salo da ƙungiyoyin siyasa ke ƙara danganta kansu da wasu mutane na musamman, maimakon jagorancin jam’iyya baki ɗaya, to APC a Katsina ya kamata ta mai da hankali.


Jam’iyyun siyasa sun fi ƙarfi ne idan magoya bayansu suka fahimci cewa shugabanninsu na iya kasancewa da muradu daban-daban, amma duk da haka suna tafiya a alkibla guda ta siyasa.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 3?