Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya samu muƙamin jagorancin shirin zaɓe na APC a Arewa maso Yamma

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TimesAbuja, 22 ga Agusta, 2026 — Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Muttaqa Rabe Darma a matsayin Daraktan shiyya na Arewa maso Yamma mai…

Katsina City News August 22, 2026  ·  12:00 AM
| 49 Views
Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya samu muƙamin jagorancin shirin zaɓe na APC a Arewa maso Yamma
Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya samu muƙamin jagorancin shirin zaɓe na APC a Arewa maso Yamma


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Abuja, 22 ga Agusta, 2026 — 


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Muttaqa Rabe Darma a matsayin Daraktan shiyya na Arewa maso Yamma mai kula da tsare-tsare, daidaita harkoki da sa ido kan zaɓe a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a shirye-shiryen zaɓen 2027.


An bayyana naɗin nasa ne cikin jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da aka fitar ranar Asabar.


Shugaba Tinubu ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai kasance mataimakinsa. Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, shi ma zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.


Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, an naɗa shi Darakta-Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance sakataren kwamitin.


A bangaren shirin zaɓe na Arewa maso Yamma, Injiniya Muttaqa Rabe Darma zai jagoranci harkokin shiyya ƙarƙashin kulawar James Abiodun Faleke, wanda aka naɗa Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tsare-tsaren zaɓe, daidaita harkoki da sa ido.


Sauran daraktocin shiyyoyin da aka naɗa sun haɗa da Sanata Olushola Adeyeye na Kudu maso Yamma; Dakta Ngozi Olejeme na Kudu maso Kudu; Sanata Uche Ekwunife na Kudu maso Gabas; Ahmed Muhammed Ketso na Arewa ta Tsakiya; da Sanata Sani Danladi na Arewa maso Gabas.


Advertisement

NRS Gateway

Haka kuma, an naɗa Sanata Adams Oshiomhole a matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tattara magoya baya, yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa zai kasance Mataimakin Darakta-Janar mai kula da harkokin gudanarwa.


Muiz Adeyemi Banire ne zai jagoranci sashen shari’a, yayin da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, zai kasance Daraktan daidaita harkokin yaɗa labarai da sadarwa ta dabaru.


Daga cikin waɗanda aka ɗora wa nauyin harkokin yaɗa labarai akwai Dele Alake, Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu. Haka kuma, an naɗa masu magana da yawun kamfen guda biyar, ƙarƙashin jagorancin Dele Alake.


Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen 2027.


Ya kuma buƙaci shugabannin sassa daban-daban na kwamitin da su bai wa sauran ’yan jam’iyyar da ba a saka sunayensu cikin kwamitin ba damar shiga cikin ayyukan kamfen.


A cikin sanarwar da Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, ya fitar, an bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ce kamfen ɗin APC zai mayar da hankali kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kuma manufofinta na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.


Ya ce ya kamata jam’iyyar ta bayyana wa ’yan Najeriya irin matakan da gwamnati ta ɗauka tare da samar da fata da kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin ƙasar.


Naɗa mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara tsananta shirye-shiryensu gabanin babban zaɓen 2027.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 2?