Za Mu Yi Maganin Ta’addanci Komai Tsawon Lokaci — Ribadu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30072025_064100_FB_IMG_1753853975737.jpg



Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta bari batun tsaron yankin Arewa ya koma siyasa ba. A cewarsa, yaki da ta’addanci aiki ne na ƙasa baki ɗaya, ba na jam’iyya, ƙabila ko yanki ba.

Ribadu ya bayyana haka ne a taron Sir Ahmadu Bello Foundation da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce gwamnati tana ci gaba da murkushe ’yan ta’adda da masu tada ƙayar baya a duk sassan ƙasar. “Muna kallon ku, mun san inda kuke, kuma ba za mu daina ba sai mun kawar da ku gaba ɗaya,” in ji shi.

Ya kuma ce duk da cewa wasu na kokarin siyasantar da batun tsaro, gwamnati ba za ta shiga wannan tarkon ba. “Idan ba a gane kokarin mu yanzu ba, tarihi zai tabbatar da gaskiya,” Inji Ribadu.

Follow Us