Shugaban Karamar Hukumar Katsina Ya Jagoranci Taron Yaye Dalibai 70 Da Ya Dauki Nauyin Koya Masu Aikin Haɗa Sola.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30072025_162717_FB_IMG_1753892755001.jpg


‎Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times.
‎Shugaban karamar hukumar Katsina Hon. Isa Miqdad Ad Saude, a cigaba da yake yi na kokarin samar wa matasan jihar Katsina aikin dogaro da kai. Ya jagoranci yaye dalibai akalla Mutum 70 wadanda ya dauki nauyin koya masu aikin hada sola, tare da yi masu kyauta ta kayan aikin domin dogaro da kai.
‎Taron ya gudana ne a ranar Laraba 30 ga watan Yuli na shekarar 2025, a dakin taro na "Multi-purpose Women Centre Katsina", inda ya samu halartar, wakilin magajin gari, dan majalissar jiha mai wakiltar Katsina, shugaban jam'iyar APC na karamar hukumar Katsina, kansiloli da shugabanin jam'iya a matakin mazabu, 
‎Shugaban kamfanin "Next Innovative Hub" Engr Abdulqadir Albaba, wanda ya jagoranci horar da matasan na tsawon wata guda, yayi jinjina ta musamman ga shugaban karamar hukumar ta Katsina wajen kokarin da yayi na samar wa matasan gurbin koyon yadda ake hada solar tare da yi masu kyautar kayan aikin solar domin dogaro da kai.
‎"Mun dauki tsawon wata guda muna koyar da wadannan matasan wannan aikin na hada sola, kuma Alhamdulillah yau gashi an kawo ranar da za'a yaye su tare da basu kyautar kayan aikin gyaran solar" ya kara da cewa "Aikin sola aiki ne wanda idan mutum ya rike shi to zai samu rufin asiri, tunda muma gashi nan cikin shi muka taso har muka zama haka". inji shi.
‎Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon. Ali Abu Albaba. Ya yaba wa shugaban hukumar hukumar wajen kokarin da yake yi na samar ma matasan jihar aikin yi domin su dogara da kai su.
‎Ya kara da cewa "Kowa yasan irin yanayin da ake ciki na rashin wadattaciyar wutar lantarki, wanda kowa hankalin shi ya fara komawa wajen kokarin mallakar sola, to cikin ikon Allah yau gashi an horas da matasa wajen yadda zasu hada solar da kuma gyarata idan ta samu matsala" inji shi.
‎A nashi jawabin kuwa, shugaban karamar hukumar ta Katsina, Isa Miqdad Ad Saude ya bayyana cewa tun asalin yadda suka shirya horaswar sun samar da hanyar da mutum zai cike bukatar neman gurbin koyarwar ta yanar gizo domin aba mutanen da suka cancanta dama.
‎"Wadannan mutanen rabi da kwatar su ban taba ganin su ba sai a yau, dalili kuwa shine mun samar da hanyar da mutum zai nemi gurbin koyarwar ne ya yanar gizo, babu bukatar sai kasan Isa Miqdad sannan ka samu wani tallafi daga karamar hukumar Katsina" inji shi.
‎Ya kara da cewa "A karkashin jagorancina zamu cigaba da yin abubuwan tallafa ma al'umma a faifai ba tare da boyo ba, muna kira da kowa da kuwa yazo ya amfana da irin ayyukan cigaba da muke kawowa karamar hukumar Katsina. Inji shi..

Follow Us