Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES
A yayin da Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ke bikin cika shekaru 70 da kafuwa, reshen Katsina na ƙungiyar ya jinjina wa ƙwararrun ’yan jarida da suka taka rawar gani tun kafin samun ’yancin kai har zuwa dorewar dimokuraɗiyya a ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar a jihar Katsina, Mannir Dan Ali, ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar tunawa da kafuwar NUJ, inda ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne a shekarar 1955 a tsakiyar gwagwarmayar neman ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.
“Wannan abu ne da tarihi ya tabbatar da shi, cewa waɗanda suka fara aikin jarida a wancan lokacin sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Najeriya ta samu ’yancin kanta a shekarar 1960,” in ji Dan Ali.
Ya bayyana cewa shekaru 70 da kafuwar NUJ sun kasance na gwagwarmaya, gaskiya, da hidima ga al’umma da ci gaban ƙasa, tare da jaddada cewa aikin jarida ba zai taɓa rasa matsayinsa na farko a cikin masu fafutukar dimokuraɗiyya ba.
“Tun daga kafuwar demokuraɗiyya a 1999 har zuwa yau shekaru 26, duk da irin rawar da ’yan siyasa, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki suka taka, aikin jarida bai da tamka,” in ji shi.
Dan Ali ya kuma waiwaya tarihinta NUJ reshen Katsina, wadda aka kafa a hukumance a shekarar 1987 bayan kirkiro da jihar Katsina. Ya yabawa shugabannin da suka gabata bisa kyakkyawan tubalin da suka kafa, wanda ya ba ƙungiyar damar ci gaba da ƙarfafa aiki har zuwa yau.
Ya ce tun lokacin da ya hau shugabancin ƙungiyar fiye da shekaru biyar da suka gabata, NUJ ta Katsina tana gudanar da muhimman taruka da shirye-shirye masu amfani ga mambobinta, inda ya yabawa goyon bayan da suke samu daga ’yan jarida da masu ruwa da tsaki.
Ya kuma gode wa dukkan ’yan jarida a Katsina daga kafafen jaridu, rediyo, talabijin, har da kafafen sada zumunta – bisa ƙoƙari da kishin da suke nuna wa aikin jarida.
A yayin bikin NUJ@70, an gabatar da wata muhimmiyar Lakca mai taken: “NUJ a Shekaru 70: Duba na Tarihi” wadda fitaccen ɗan jarida kuma malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Katsina, Dr. Sama'ila Balarabe, ya gabatar. Dr. Balarabe ya taɓa yin aiki a Gidan Rediyon Katsina kuma ya shugabanci Ƙungiyar NUJ a lokacin.
Taron ya samu karin haske daga manyan shugabannin ƙungiyar da suka taba jagorancin ta, ciki har da tsohon shugaban NUJ Katsina, Mansir Kaware, tsohon sakataren shiyyar Arewa na kungiyar NUJ, Abdullahi Izma Yamadi, Muhammad Danjuma Katsina mawallafin KatsinaTimes, Abdullahi Aliyu Yar'adua Sakataren Yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, da bangarorin jami'an tsaro.
Dan Ali ya buƙaci mahalarta da su yi nazari akan Lakca da da kyau, domin tana da alfanun zurfafa fahimta da ƙarfafa ƙima da tarihin ƙungiyar NUJ.
Ya kammala da nuna godiya ga duk wanda ya halarta, tare da fatan Allah ya sa a kammala taron lafiya da nasara.