Katsina Times
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dutsin-Ma da Kurfi, Hon. Aminu Balele Kurfi wanda aka fi sani da “Dan Arewa”, ya kai ziyarar jaje ga al’ummar Gobirawa da ke cikin gundumar Kuki a karamar hukumar Dutsin-Ma, Jihar Katsina.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Laraba, sakamakon wani mummunan ibtila’i da ya auku a yankin, wanda ya janyo asarar rayuka da lalacewar dukiyoyi.
Yayin ziyarar tasa, Hon. Balele ya bayyana alhininsa tare da jajanta wa mazauna yankin, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatin tarayya da jiha suna aiki tukuru domin inganta harkar tsaro a yankunan da abin ya shafa. Ya ce akwai ayyukan da ake aiwatarwa da ba lallai ne a bayyana su a fili ba saboda dalilai na tsaro.
Al’ummar Gobirawa sun nemi tallafi musamman a fannin hasken wuta da wasu bukatun rayuwa. Nan take, Hon. Balele ya umarci mataimakin shugaban karamar hukumar da ya gaggauta daukar mataki, sannan ya bayar da tallafin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari uku (N1.3m) domin taimakawa wadanda iftila’in ya shafa.
Bayan kammala wannan ziyara, Hon. Balele ya ci gaba da zagayawa wasu ƙauyuka da ke cikin yankin Kuki a cikin daren, domin gaisuwar jaje da daukar nauyin tallafin gaggawa. Al’umma da dama sun bayyana farin cikinsu da godiya kan irin kulawar da ya nuna, suna masa fatan alheri da fatan Allah ya saka masa da mafificin sakamako.