Tsofaffin 'yantakarkarin jam'iyyar PDP a Katsina sun yi mubayi'a ga tafiyar "Coalition Sabuwar Tafiya".

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20062025_131129_FB_IMG_1750425007014.jpg

Auwal Isah Musa | KatsinaTimes 

Tsofaffin 'yantakarkari daga jam'iyyar PDP wadanda suka fito daga kananan hukumomi daban-daban na jihar Katsina a matakan Kansiloli, Ciyamomi da 'yanmajalissa, sun mika akalarsu ga Tafiyar Hadaka ta su Dr. Mustapha Inuwa mai suna "Coaliation Sabuwar Tafiya."

Taron mubayi'ar tsaffin 'yantakarkarin da suka hada da tsaffin 'yanmalissun tarayya 25, Ciyamomi 10 da Kansiloli 220, ya gudana ne a ranar 19 ga Yuni, 2025 a ofishin jagoran tafiyar, Dr. Mustapha Inuwa da ke hanyar zuwa Mani.

Da yake jawabin kan dalilinsu na barin jam'iyyar ta PDP zuwa sabuwar tafiyar hadakar, shugaban tawagar tsaffin 'yantakarkarin Majalissu, Honorabul Jamilu Yahaya Kankara, ya bayyana rashin adalcin da aka yi masu a zabukan shekarar 2023 a matsayin manyan dalilai.

 "Kadan daga dalilin da ya sa muka baro waccan tafiyar ta PDP muka taho mu yi hadaka ta musamman da wannan sabuwar tafiya shi ne sakaci, yaudara da karairayin da ake yi a jam'iyyar PDP."

Ya ce, su manya a jam'iyyar PDP sun rika wasan kura da su saboda wani buri daban na kashin kansu, a maimakon burin a zo a kafa gwamnati. Ya kara da cewar, su kima tun da suna hankali, Ilimi da sanin ya kamata, shi ya sa suka yanke shawarar yin hadaka da tafiyar ta su Dr. Musyapha Inuwa, domin a ganinsu ita ce tafiya mai ma'ana, ba shirita da wasa ba.

Da yake jawabin karbar mubayi'ar tasu, jagoran tafiyar "Coalition Sabuwar Tafiya", Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, ya nuna farin cikinsa bisa yarda da amincewarsu da sabuwar tafiyar tasa, inda ya bayyana su a matsayin wadanda suka gane gaskiya ., daga nan ne kuma ya bayyana su a matsayin wadanda za su kasance cikin kwamitin ayyukan tafiyar a matakin  jiha da kasa baki daya.

"Daga wannan lokacin kun zama cikin duk wani Kwamiti da ake zama ana tattaunawa al'amurran nan. In kun wakilci mutanenku da kyau ruwanku, in ba ku wakilce su da kyau ba; ku ne. Mu dai mun fita!"

Daga karshe, Dr. Mustapha Inuwa ya hore su da su yi aiki a tafiyar da zuciya daya, hadin tare da fid da son kai, inda ya ce "son kai ne ya kai shugabancin kasar nan inda take yanzu."

Mu'abayi'ar tasu, ta samu karbar jagoran tafiyar, Dr. Mustapha Inuwa da masu dafa masa da suka hada: Sanata Ahmad Babba Kaita, Honorabul Salisu Lawal Uli, Hajiya Amina Mani, Ambasada Yakubu Muhammad da sauransu.

Follow Us