Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama 'yan rundunar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, wato Super Falcons, da kyautar karramawa ta ƙasa da kuma kyautar kuɗi da ta gidan kwana saboda nasarar su a gasar Kofin Ƙasashen Afrika na Mata (WAFCON), wanda aka gama ranar Asabar, inda suka ciyo kofin a karo na 10.
A wurin wata babbar walima da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Dutsen Aso a ranar Litinin, Tinubu ya ba da lambar girma ta ƙasa ta Officer of the Order of the Niger (OON) ga kowace daga cikin 'yan wasan su 24.
Haka kuma ya gwangwaje kowace 'yar wasa da kyautar tsabar kuɗi Naira wadda ta yi daidai da Dalar Amurka dubu ɗari ($100,000), da kuma gida mai dakunan kwana uku.
Bugu da ƙari, kowanne daga cikin ma'aikatan kulob ɗin ƙwallon ƙafar an ba shi kyautar dala dubu hamsin ($50,000) (a naira), a matsayin godiya saboda muhimmiyar rawar da suka taka wajen samun nasarar.
“Wannan ƙungiya ta ƙara janyo wa Nijeriya abin alfahari a duniya," inji Tinubu. “Jajircewar ku da zummar ku da wasan ku sun kasance abin koyo ba kawai ga 'yan wasa masu tasowa ba har ma ga kowane ɗan Nijeriya.
“Na karɓi wannan kofi a madadin dukkanin 'yan Nijeriya, kuma na ce maku: mun gode da sadaukarwar ku da hoɓɓasan ku, da kuma tuna mana da ƙarfin halin 'yan Nijeriya da kuka yi.
“A madadin ƙasar nan da ke cike da godiya, a nan ina bai wa dukkan 'yan wasa da ma'aikatan kulob su 11 kyautar karramawa ta ƙasa mai suna 'Officer of the Order of the Niger' (OON).
“Bugu da ƙari, ina ba da umurnin cewa a ba kowace 'yar wasa da kowane ma'aikacin kulob kyautar gida mai daki uku.
“Wani ƙari kuma shi ne, akwai kyautar tsabar kuɗi a naira wadda ta yi daidai da $100,000 ga kowacce daga cikin 'yan wasa 24, da kuɗi da ya yi daidai da $50,000 ga kowanne daga cikin ma'aikatan kulob su 11.
“Ina ƙara taya ku murna, kuma zan ci gaba da yi maku addu'a. Da wannan, ruhin Nijeriya ba zai gaza ba kuma ba zai taɓa mutuwa ba.”
Shugaban Ƙasar ya ba da labarin yadda mutane suka riƙa ji a ran su lokacin da wasan ya zo kusan ƙarshe, yana mai nuni da yadda wasan da 'yan wasan suka riƙa bugawa ya daga ruhin ƙasar nan tare da haɗa kan 'yan Nijeriya a duk inda suke.
Ya ce: “Nasarar ku tana wakilta abin da ya na zarce nasara a wasa. Nasara ce ta bajinta, jajircewa, ɗa'a, da kuma tsayawa kai da fata.
“A gaskiya, da farko ban so na kalli wasan. Ban so na samu hawan jini. Amma sai mutane suka shigo suka kamo tashar da ake wasan a talbijin ɗina. Lokacin da aka ci 2-0, sai rai na ya ɓaci , na rasa sukuni.
“Amma ina dai ta kallo da ƙarfin zuciya, da dagewa, da bajinta. To bayan an buga fanariti ɗin nan, sai na ji ƙarfi a rai na, kuma na yi amanna da cewa shi ma ran ƙasar nan ya ƙarfafa.
“Amma fa kun kusa sanya ni na yi ƙarin fushi domin mamar ku (wato Uwargidan Shugaban Ƙasa) tana cikin ɗakin girki, ta kusa mantawa da abinci na.
”Ba ta kallon gasar sai idan namu 'yan matan ne suka buga wasa. To lokacin da aka busa usur ɗin ƙarshe, sai duk aka ɓarke da murna a duk faɗin ƙasar nan."
Shugaban Ƙasa ya tabbatar wa da kulob ɗin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ba su goyon baya da kuma mara wa cigaban harkokin wasanni baya, tare da alƙawarin cewa gwamnatin za ta ƙara zuba jari a harkar ƙwallon ƙafar mata da cigaban matasa a duk faɗin ƙasar nan.
Ya ce: “Labarin ku labari ne na kyakkyawar fata. Don haka a wannan zamani na Sabunta Kyakkyawar Fata (Renewed Hope), muna taya ku bikin murna ba kawai a matsayin ku na zakarun Afrika ba, har ma gwarzayen mafarkin Nijeriya.”
Wani ƙarin godiya shi ne Shugaban Ƙungiyar a Gwamnonin Nijeriya (NGF), wato Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, shi ma ya bayyana kyautar naira miliyan goma (₦10m) ga kowace 'yar wasa da ma'aikatan kulob ɗin a madadin gwamnoni jihohi 36.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana 'yan wasan Super Falcons a matsayin abin koyi kuma kyakkyawan misalin bajinta da inganci.
Ta taya su murna saboda wasa mai jan hankali da suka yi da kuma ƙarfin ruhin su, tana mai bayyana aikin su da cewa “alama ce ta dagewa, aiki tare, da jajircewa."
Kyaftin ɗin Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce nasarar da su ta kulob ɗin su ce kuma ta kowace yarinya 'yar Nijeriya ce da ke mafarkin cimma wani gagarumin abu a rayuwa.
Ta ce: “A yau, na tsaya a gaban ku ba kawai a matsayin kyaftin ɗin Super Falcons ba, har ma a matsayin ɗiyar Nijeriya mai alfahari, ɗauke da mafarkai, jajircewa, da ruhin babbar ƙasar mu.
“A madadin ƙawayen aiki na, koci-kocin mu, da ma'aikatan mu, ina bayyana godiyar mu saboda wannan kyakkyawar tarba da aka yi mana da kuma nagartacciyar amannar da kuka nuna mana.”
Da take nanata muhimmancin cin kofin na 10 na gasar WAFCON da suka yi, kyaftin ɗin ta ce: “Wannan nasara ba kurum a kofi take ba. Shaida ce ta rashin gazawar ruhin Nijeriya. Abin murna ne ga kowace ƙaramar yarinya da ke ƙauyukan mu, garuruwan mu, da biranen mu wadda ke da ƙoƙarin yin mafarki... Wannan cin kofin na 10 naka ne, ya mai girma Shugaban Ƙasa, na 'yan Nijeriya ne, na Nigerians, Super Falcons, Kuma na kowane ƙaramin yaro da ya yi amanna tare da mafarkin zai hau wannan dandamalin wata rana."