Gwamnatin Tinubu Ta Kama Ton 5,545 na Miyagun Ƙwayoyi da Masu Safara 40,000 – Buba Marwa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30072025_064611_Buba-Marwa.jpg


Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana cewa tun daga zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Mayun 2023 zuwa yanzu, an samu gagarumar nasara wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Buba Marwa ya bayyana cewa hukumar NDLEA ta kama ton 5,545 na miyagun ƙwayoyi, wanda yake daidai da tireloli 200. Ya bayyana cewa “Mun kama mutane sama da 40,000 da ake zargi da hannu a safarar ƙwayoyi, sannan an yanke hukunci kan mutane 8,600, yayin da sama da mutane 24,000 suka sauya tunani bayan samun shawarwari da gyaran hali.”

A bangaren wayar da kai, Marwa ya bayyana cewa hukumar ta gudanar da shirye-shiryen faɗakarwa a wurare sama da 8,000, ciki har da wuraren shakatawa, tashoshin mota, makarantu, kasuwanni, Masallatai da Majami’u. Wannan shiri, a cewarsa, an yi shi ne domin fadakar da jama’a musamman matasa game da haɗarin shan miyagun ƙwayoyi.

A cewar Marwa, “Shugaban ƙasa ya amince da kafuwar cibiyoyin gyaran tarbiyya da tunani guda bakwai, kuma a wannan shekara muna da niyyar ƙara wasu 30 domin kowace jiha ta samu cibiyar gyara hali da dawo da wadanda suka fada tarkon shaye-shaye.”

Har ila yau, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa amincewa da gina sabbin cibiyoyi na zamani da zasu taimaka wajen gudanar da shirin yakar shaye-shaye da kuma hana fataucin ƙwayoyi. Ya ce wannan na daga cikin manyan sauye-sauyen da za su taimaka wajen samar da lafiyayyar al’umma a Najeriya.

Buba Marwa ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Tinubu na ci gaba da wannan aiki ba tare da sassauci ba, domin kare matasa da makomar ƙasa daga barazanar miyagun ƙwayoyi.

Follow Us