Shugaba Tinubu Ya Fito Da Sabbin Tsare-Tsare Don Inganta Tattalin Arzikin Najeriya – Atiku Bagudu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30072025_113243_bagudu2.jpg

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da tsare-tsaren da za su sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya, da cika alkawuran da aka dauka ga ’yan Najeriya musamman yankin Arewa. Ya bayyana hakan ne a wurin zaman farko na rana ta biyu a taron kwanaki biyu na Cibiyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation), da aka gudanar na tattaunawa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa.

Bagudu ya bayyana cewa tsarin “Renewed Hope Agenda” da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, ya mayar da hankali kan manyan abubuwan da suka shafi cigaban ƙasa, ciki har da tsaro, ilimi, noma, kiwon lafiya da kuma sabunta ginshikan tattalin arziki. Ya ce: “Shugaban Ƙasa yana da cikakken imani da Najeriya. Ba ya yanke hukunci bisa kabila ko yanki. Ya dora gwamnatin sa bisa adalci da gamsarwa.”

Ministan ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu ta janye tallafin mai da kuma aiwatar da sauye-sauye a fannin hada-hadar kudin waje (foreign exchange reform), wanda hakan ya ba da dama ga karin kudaden shiga ga jihohi da ƙananan hukumomi. Bagudu ya bayar da misali da jihar Jigawa inda bashin da ake bin ta ya ragu daga biliyan 43 zuwa kasa da biliyan daya a cikin shekaru biyu. “Wannan sauyi ne na tarihi da bai taba faruwa ba,” in ji shi.

A karshe, Bagudu ya bukaci Arewa da ta ci gaba da mara wa gwamnatin Tinubu baya domin ci gaban kasa baki daya. Ya ce, “Mun zabi Asiwaju Bola Tinubu ne da kuri’u mafi yawa, ba iya a babban zaɓe ba, har a zaɓen fidda gwani. Yanzu lokaci ne na goyon bayan hadin kai, ci gaba, da tabbatar da cewa mu ne ginshikin cigaban Najeriya. Gwamnatin nan tamu ce, kuma ta dukkan ’yan Najeriya ce.”

Taron wanda ya tara manyan jami’an gwamnati da shugabannin al’umma daga sassa daban-daban na ƙasa, ya zama wani dandalin bayyana nasarorin gwamnati da kuma lalubo hanyoyin inganta haɗin kai da fahimta tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa.

Follow Us