Taron TETFund: Dole ne a samar da digiri mai amfani wajen gina al’umma – Farfesa Sagir Adam Abbas

Daga wakilanmu | Katsina TimesTsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sagir Adam Abbas, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a sake fasalin tsarin karatun digiri a…

Katsina City News October 16, 2026  ·  12:00 AM
| 75 Views
Taron TETFund: Dole ne a samar da digiri mai amfani wajen gina al’umma – Farfesa Sagir Adam Abbas
Taron TETFund: Dole ne a samar da digiri mai amfani wajen gina al’umma – Farfesa Sagir Adam Abbas


Daga wakilanmu | Katsina Times

Tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sagir Adam Abbas, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a sake fasalin tsarin karatun digiri a jami’o’in Najeriya, domin ya dace da yanayin zamani tare da samar da ilimin da zai amfani al’umma.

Farfesa Abbas ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na Hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu ta Ƙasa (TETFund), wanda aka gudanar a Abuja, inda ya gabatar da takarda mai taken “From Degrees to Development: Are Nigerian Universities Producing the Human Capital Nigeria Needs?” (Daga Digiri zuwa Ci Gaba: Shin Jami’o’in Najeriya Suna Samar da Ƙwararrun Ma’aikatan da Ƙasar ke Buƙata?).

A cikin takardar tasa, Farfesan ya bayyana damuwarsa kan yadda digiri ya zama kamar wata takardar shedar cancanta kawai, inda ake ta ƙoƙarin yaye ɗalibai daga jami’o’i a kowace shekara, yayin da dubban matasa kuma ke fafutukar samun gurbin karatu domin su mallaki wannan sheda.

Ya jaddada cewa wajibi ne a sake duba tsarin karatun jami’o’i, ta yadda ilimin da ɗalibai ke samu zai taimaka musu wajen dogaro da kansu, samar da ayyukan yi da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma.

Farfesa Abbas ya ƙara da cewa, bisa la’akari da yadda duniya ke sauyawa cikin sauri, lokaci ya yi da jami’o’in Najeriya za su haɗa karatunsu da buƙatun masana’antu, kamfanoni da cibiyoyin kasuwanci, domin ɗalibai su kammala karatu da ƙwarewar da za ta ba su damar tunkarar ƙalubalen rayuwa.

Advertisement

NRS Gateway

A yayin tattaunawar da ta biyo bayan gabatar da takardar, ɗaya daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa, saboda muhimmancin batutuwan da Farfesa Abbas ya gabatar, ya kamata a sake gabatar da takardar a wani babban taro da zai samu halartar shugaban ƙasa da mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, domin su fahimci halin da tsarin ilimin jami’o’i ke ciki da kuma buƙatar sake fasalinsa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Jami’ar Sufuri ta Daura, Farfesa Umar Adam Katsayal, ya bayyana cewa jami’arsu ta tsara tsarin karatu da zai bai wa ɗalibai damar samun ƙwarewa ta hanyar hulɗa da kamfanoni da wuraren sana’o’i da suka dace da fannonin karatunsu.

Ya ce wannan tsari zai taimaka wajen tabbatar da cewa ɗaliban da suka kammala karatu ba su tsaya ga samun takardar digiri kawai ba, sai dai sun mallaki ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun ayyukan yi ko kafa sana’o’insu.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron tare da sauraron wannan muhimmin jawabi akwai Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda; Ministar Ilimi; shugabannin manyan makarantu daban-daban a Najeriya; wakilan ƙungiyoyin farar hula da malaman addinin Musulunci.

Jawabin Farfesa Abbas ya sake jaddada muhimmancin sake fasalin tsarin ilimin jami’o’i a Najeriya, ta yadda za a mayar da hankali kan samar da ƙwararrun ma’aikata, bunƙasa sana’o’i da kuma amfani da ilimi wajen magance matsalolin al’umma.

Domin karanta cikakkiyar takardar cikin harshen Turanci, a ziyarci shafin Katsina Times ta adireshin: www.katsinatimes.com.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 4?