An saka ranar 27 ga Nuwamba domin shari’ar APC da wasu ’yan takara a jihar Katsina

Muazu Hassan @ Katsina TimesAlkalin Babbar Kotun Tarayya ta 1 da ke jihar Katsina, Mai Shari’a Aminu B. Aliyu, ya saka ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, domin sauraren karar…

Katsina City News November 12, 2026  ·  12:00 AM
| 84 Views
An saka ranar 27 ga Nuwamba domin shari’ar APC da wasu ’yan takara a jihar Katsina
An saka ranar 27 ga Nuwamba domin shari’ar APC da wasu ’yan takara a jihar Katsina


Muazu Hassan @ Katsina Times


Alkalin Babbar Kotun Tarayya ta 1 da ke jihar Katsina, Mai Shari’a Aminu B. Aliyu, ya saka ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, domin sauraren karar da jam’iyyar APC ta jihar Katsina ta shigar a kan wasu da suka samu takara a wasu jam’iyyun.


APC ta kai karar ne bisa hujjar cewa waɗanda aka ba tikitin takara, waɗanda suka fito daga cikin jam’iyyun PDP, ADC da APM, ba su cancanci tsayawa takara ba bisa wasu ƙa’idojin da dokar zaɓe ta tanada ta shekarar 2027.

Hujjojin sun haɗa da cewa waɗanda suka samu tikitin takarar sun same su ne bayan wa’adin da hukumar zaɓe ta bayar na gabatar da sunayen dukkan ’yan jam iyya  ya ƙare.


Haka kuma, ba za ka iya tsayawa takara ba sai kana ɗan jam’iyya, sannan sunanka yana cikin kundin sunayen ’yan jam’iyyar da ke rumbun adana bayanai na hukumar zaɓe.


Advertisement

NRS Gateway

Biyu daga cikin waɗanda shari’ar ta shafa sun bayyana wa jaridun Katsina Times cewa lamarin ya zo musu da mamaki, amma sun shirya tunkararsa.


Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page; katsina city news 

Facebook group. Katsina city news 

Facebook page. Jaridar taskar labarai

All social media handles @ katsina times 

07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 3 + 4?