Najeriya: Sabon Rahoton Amnesty akan Hakkin Dan’adam

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29042025_221527_FB_IMG_1745964808888.jpg

An kama ƴan jarida da masu sharhi a kan mahukunta da aka caje su kuma aka tsare su ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun kama tare da cuzguna wa masu zanga-zanga, kuma sun yi amfani da ƙarfi fiye da kima wajen daƙushe zanga-zangar, wanda ya haifar da mutuwar masu zanga-zangar da dama. An kashe ɗaruruwan mutane a tashin hankali. Ƴan mata da Boko Haram suka sake suna ci gaba da zama cikin rashin tallafi da adalci. Wata kotu a Burtaniya ta ba wa al’ummomi a jihar Rivers damar tuhumar kamfanin Shell da alhakin lalacewar muhalli.

MATASHIYA
Ambaliyar ruwa a jihohi 33 ta hallaka mutane fiye da 300 kuma ta yi sanadiyyar gudun hijira ga dubban mutane. Ruwa ya malale fiye da hekta 61,000 na ƙasa a jihar Kogi. Haka kuma a jihar Borno, ambaliyar ruwa ta hana samun agajin jinƙai ga mutane 27,000. A jihar Borno, an gano yara 1,618 masu fama da rashin abinci mai gina jiki tsakanin tsakiyar watan Mayu zuwa Yuni saboda tsadar farashin kayan abinci, da kuma rashin isasshen tsaftar muhalli. Tun daga tsakiyar watan Oktoba, an sami fiye da mutum 14,000 da cutar kwalara, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutum 378.

ƳANCIN FAƊAN ALBARKACIN BAKI
A ranar 23 ga watan Yuli ne Majalisar Wakilai ta gabatar da ƙudurin dokar yaƙi da zagon ƙasa, wadda ta yi niyyar sanya tsauraran hukunci ga ƴan Nijeriya da suka kasa karanta sabon taken ƙasa da aka amince da shi, ko kuma waɗanda suka soki ƴan siyasa ko shugabannin al’umma. Ƙudurin Dokar ya wuce karatun farko kuma ya ci gaba zuwa na biyu, amma a ranar 14 ga watan Agusta kakakin Majalisar ya janye bayan koken jama’a.
Hukumomi sun ci gaba da kamawa da tsare ƴan jarida da sauran masu nuna ra’ayoyi da suka saɓa da na gwamnati. A ranar 15 ga watan Maris, jami’an rundunar sojin Nijeriya sun sace ɗan jarida Segun Olatunji na jaridar intanet The First News a gidansa. Wannan ya faru ne saboda wani labarin da ya rubuta yana zargin wani jami’in hukumar tsaro ta Nijeriya (NDIA) da fifita danginsa a wajen aiki. Bayan matsin lamba na jama’a, jami’an NDIA sun amince da cewa suna tsare shi kuma sun sake shi a ranar 28 ga watan Maris.
A ranar 1 ga watan Mayu, Daniyel Ojukwu, ɗan jarida da ke aiki tare da Gidauniyar Bincike na Jarida (FIJ) ‘yan sanda sun sace shi kuma sun tsare shi. Wannan ya faru ne bayan da ya ruwaito cewa Adejoke Orelope- Adefulire, babbar mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan manufofin ci gaba mai ɗorewa, ya biya Naira miliyan 147 (Dala 106,154) a cikin asusun bankin wani gidan abinci. An biya kuɗin ne daga kuɗin hukuma da aka ware don ginin makaranta. An saki Daniyel Ojukwu bayan kwanaki 10 bayan wani kuka da jama’a suka yi. A ranar 14 ga watan Agusta ,an tsare Fisayo Soyombo, babban edita na Gidauniyar Bincike na Jarida, a kan wannan rahoto. An sake shi daga baya a wannan rana a kan sharaɗi.
A ranar 29 ga watan Agusta, ƴan sanda sun kama ɗan jarida Muktar Dahiru saboda wani saƙon Facebook da ake ganin “zagi” ne ga Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano. An tuhume shi da laifin haɗin-baki, ɓata suna da zagi da gangan.
Ranar 29 ga watan Mayu wata babbar kotun tarayya a Abuja Babban Birnin Tarayya ta tura Chioma Okoli kurkuku bayan da aka tuhume ta da laifin ɓata-suna a ƙarƙashin dokar cin zarafi a yanar gizo. Chioma Okoli ta wallafa a Facebook cewa tumaturin gwangwani da Erisco Foods Ltd yake samarwa yana ɗauke da sukari mai cutarwa. An sake ta a ranar 31 ga watan Mayu a kan tsauraran sharuɗɗan beli. Ana ci gaba da shari’arta a ƙarshen shekara.
A ranar 27 ga watan Mayu, ƴan sanda sun kama Eze Chukwunonso, mai wallafa jarida News Platform ta intanet aka kuma tsare shi har tsawon kwanaki 18. Ya rubuta wata ƙasida da ke zargin cewa wani ɗan

kasuwa ya yi rikici da wani maƙwabcinsa a wani rukunin gidaje a Legas, a inda aka yi harbe-harbe. Yana fuskantar zargin aikata laifuka na “halin da zai iya haifar da keta zaman lafiya, ko yake haifar da keta zaman lafiya ta hanyar wallafe-wallafe mai banƙyama, da kuma maƙarƙashiya don aikata laifuka”.

KAMAWA DA TSAREWA BA BISA ƘA’IDA BA
A ranar 8 ga watan Agusta, ƴan sanda sun kai samame a hedkwatar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC). A ranar 19 ga watan Agusta, Hukumar Tsaro ta DSS ta kira Joe Ajaero, shugaban NLC , don amsa tambayoyi game da zargin laifin haɗin-baki da tallafiwa ta’addanci da cin amanar ƙasa da zagon-ƙasa da kuma laifukan intanet. A ranar 9 ga watan Satumba ne jami’an DSS suka kama Joe Ajaero a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya.

ƳANCIN TARON LUMANA
Gwamnati ta sanya takunkumin da ba bisa ƙa’ida ba kan haƙƙokin yin taron lumana da hadin kai. Bayan zanga-zangar #EndBadGovernance daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta, an tsare mutane fiye da 1,000 a faɗin ƙasar kuma aƙalla masu zanga-zangar 24 sun mutu a tashin hankali da jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kano da Maiduguri da jihohin Jigawa, Katsina, Nijar da Kaduna.1
A ranar 2 ga watan Satumba ne hukumomi suka gurfanar da masu zanga-zangar #EndBadGovernance su 12: Adeyemi Abiodun Abayomi, Musa Abdullahi, Michael Tobiloba Adaramoye, Bashir Bello, Angel Love Innocent, Nuradeen Khamis, Buhari Lawal, Lucky Ehis Obiyan, Mosiu Sadiq, Opaluwa Eleojo Simeon, Suleiman Yakubu da Abdulsalam Zubairu. An gurfanar da su a gaban babban kotun tarayya a Abuja kan zargin ƙarya, ciki har da cin amanar ƙasa da makirci don rikitar da Najeriya da tayar da ƙayar-baya, da kiran yaƙi da ƙasar Nijeriya.
A ranar 1 ga watan Nuwamba, bayan da aka kama su da kuma muzguna musu, an gurfanar da masu zanga-zangar #EndBadGovernance su 114 rukuni-rukuni a babbar kotun tarayya a Abuja. Yawancin waɗanda aka sanya su a ɗaya daga cikin rukunin yara ne. Huɗu daga cikin yaran sun faɗi a cikin kotun, bayan sun shafe fiye da wata biyu a tsare a cikin yanayi mai ban tsoro. A jihar Katsina, yara 12 ƴan ƙasa da shekaru 16 sun fuskanci shari’ar zalunci, inda ake zargin su da shiga zanga-zangar #EndBadGovernance.
Yawancin waɗannan yara an kama su ne kawai saboda kasancewa a kan tituna yayin zanga-zangar.2

ƳANCIN YIN GASKIYA DA ADALCI DA BIYAN DIYYA
A ranar 10 ga watan Yuli, Kotun ECOWAS ta yanke hukunci a shari’ar Obianuju Catherine Udeh da wasu mutum 2 da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya cewa hukumomin Najeriya sun keta haƙƙoƙin masu zanga- zangar #EndSARS. Haƙƙoƙin da aka keta sun haɗa da haƙƙoƙin tsaro na mutum da ƴancin faɗar albarkacin baki da taron lumana da ƙungiya, da kuma ƴancin kariya daga azabtarwa da sauran abubuwan muzgunawa, haƙƙin yin bincike na ƙasa, da kuma haƙƙin samun ingantaccen magani. Duk da haka, Kotun ta kasa riƙe hukumomin Najeriya da laifin kashe masu zanga-zangar 12 a watan Oktoba 2020 a wurare biyu: a mashigar Lekki; da kuma gundumar Alausa, jihar Legas.

HARE-HAREN DA BA BISA ƘA’IDA BA DA KISAN KAI
A cikin rahoton da aka wallafa a watan Oktoba, Amnesty International ta rubuta aƙalla mutuwar mutum 555 a cikin 363 da aka rubuta a tsakanin Janairu 2012 da Agusta 2023. Yawancin waɗanda abin ya shafa an azabtar da su har lahira ko kuma an kashe su bayan an zarge su da sata da sihiri da zagi, da sauran abubuwa. Waɗannan ƙananan abubuwan da aka bincika da kuma gurfanar da su sun nuna gazawar da hukumomi ke yi don kare mutane daga tashin hankali.3
Tsakanin Disamba 2023 da Fabrairu 2024, ƴan bindiga sun kai hari ga al’ummomi a Barkin Ladi da Bokkos da Mangu ƙananan hukumomin jihar Plateau, inda suka kashe mutane 1,336 ciki har da yara 260.

A watan Maris, wani bam ya fashe a Kawori, a ƙaramar hukumar Konduga da ke jihar Borno, inda ya kashe mutane 16 kuma ya jikkata da dama.
A watan Afrilu, manoma da makiyaya sun yi rikici a yankin karamar hukumar Omala dake jihar Kogi, wanda ya jawo mutuwar mutane 21. A watan Yuni, mutane takwas sun jikkata a wani hari da makiyaya suka kai a ƙananan hukumomin Birnin kudu da Dutse da Kiyawa a jihar Jigawa.
A ranar 24 ga watan Disamba, ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane 15 — mafi yawansu mata da yara — a wani hari ga al’ummar Gidan Ado na Ganawuri a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau, inda aka bar gawarwaki a warwatse a gidaje da gonaki.

SAƁA WA DOKOKIN AYYUKAN JINƘAI NA ƘASA DA ƘASA
A ranar 30 ga watan Satumba ne rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kai hare-haren sama a ƙauyen Jika da Kolo dake ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, inda ta kashe mazauna ƙauyen 23, ciki har da yara. Masallata a masallaci da masu sayayya a kasuwa na cikin waɗanda abin ya shafa.
A ranar 25 ga watan Disamba, harin sojan sama ya kashe aƙalla mutum 10 a cikin al’ummomin Gidan Sama da Rumtuwa a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

HAƘƘOƘIN MATA DA ƳAN MATA
Hukumomi sun gaza ɗaukar matakan da suka dace don hana kai hare-hare ga ƴan mata da makarantu. Shekaru goma tun bayan da mayaƙan Boko Haram suka sace ƴan matan makaranta 276 a Chibok, jihar Borno, 82 sun ci gaba da zama ana garkuwa da su. An tilasta wa mata ashirin daga cikin waɗanda aka sako su zauna tare da mayaƙan Boko Haram “da suka tuba” waɗanda aka tilasta musu auren su lokacin da suke tsare. An sace ƴan mata da dama a hare-haren da suka biyo baya.4
Amnesty International ta ruwaito a watan Yuni cewa ƴan matan da ke da alaƙa da Boko Haram, ko kuma ana ganin suna da alaka da su, bayan sun tsira daga shekarun cin zarafin a hannun ƴan Boko Haram da sojojin Nijeriya, an hana musu sake shiga jama’a da yi musu adalci.5
A ranar 24 ga watan Agusta, ƙudurin dokar da zai soke dokar (hana) cin zarafin mutane (2015) – dokar da aka tsara don daƙile cin zarafin jinsi a Najeriya – ya ci gaba zuwa karatu na biyu a Majalisar Dattijai.

HAƘƘOƘIN TATTALIN ARZIƘI DA ZAMANTAKEWA DA AL’ADU
Yawan hauhawar tsadar rayuwa na kashi 33.4% – wato ƙaruwar da ta kai kashi 9.32% daga watan Yulin 2023 – da kuma ƙaruwar farashin kayayyaki da ayyuka ya haifar da raguwa a yanayin rayuwar mutane. A ranar 5 ga Satumba, gwamnati ta ƙara farashin man fetur daga Naira 617 (Dala 0.37) zuwa Naira 817 (Dala 0.50) a kowace lita ba tare da samar da matakan sauƙaƙa wa rayuwa don kare kuɗaɗen shiga ba. A ranar 9 ga watan Satumba, jami’an ma’aikatar harkokin wajen ƙasar sun kutsa cikin ofishin ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama mai suna, Aikin Binciken Haƙƙoƙin Tattalin Arziki da Zamantakewa (SERAP) ba bisa ƙa’ida ba, bayan da ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasar da ya janye ƙarin farashin cikin sa’o’i 24.
Tsakanin Disamba 18-22, mutane 67 sun mutu — yawancinsu dama yunwa ta kusa kashe su — a cikin turmutsutsu, yayin da suke ƙoƙarin samun abinci lokacin ba da sadaka da raba shinkafa: a ranar 18 ga Disamba, yara 35 sun mutu a garin Ibadan a jihar Oyo. A ranar 21 ga watan Disamba, mutum 22 sun mutu a garin Okija da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra. A ranar 21 ga watan Disamba mutum 10 sun mutu a Abuja.

HAƘƘIN SAMUN LAFIYAYYEN MUHALLI
A ranar 11 ga watan Oktoba, Kotun ɗaukaka ƙara ta Burtaniya ta yanke hukuncin cewa shari’ar da al’ummomin Bille da Ogale na jihar Rivers suka gabatar a shekarar 2015 a kan kamfanin Shell ya kamata ta ci gaba zuwa cikakkiyar shari’a. Wannan mai yiwuwa zai haifar da bayyana takardun cikin gida masu

mahimmanci na kamfanin Shell. Wannan ya yi watsi da hukuncin da Babban Kotun Burtaniya ta yanke a watan Maris wanda ya hana adalci ga al’ummomin biyu da suka shigar da ƙarar don riƙe kamfanin Shell da alhakin shekaru da dama na lalacewar muhalli da ya haifar na malalar man fetur.
Amsar da Nijeriya ta yi game da sauyin yanayi bai isa ba saboda rashin kyawun manufofinta da rashin isasshen makamashin da za a iya sabuntawa.

Follow Us