Kuyi Watsi Da Duk Wata Jita-Jita Da Makiyan Cigaban Jihar Kebbi Da Jam'iyyarmu Ta APC Cewa Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Yana Shirin Komawa PDP.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30042025_151644_IMG-20250430-WA0049.jpg

Hon. Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa ("Sarkin Arawan Kabi") Yayi Allah Wadai Da Waɗanda Suka Ƙirkiri Wannan Labari Na Karya, Sunyi Hakane Domin Kawo Hargitsi Cikin Wannan Jaha Tamu.

Ɗan Takarar Sanatan Kebbi Ta Arewa Hon. Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa Yace Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Yana Nan Cikin Jam'iyyar APC Kuma Yana Tareda Shugaban Ƙasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Ɗari Bisa Ɗari.

Mu Al'ummar Jihar Kebbi Muna Nan Cikin Jam'iyyar APC Ƙarkashin Jagorancin Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Da Shugaban Ƙasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Kuma Insha Allahu Zasu Yi Nasara 2027.

Makiyan Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Da Shugaban Ƙasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Sun Karbi Ƙwangilar Kawo Rikici A Wannan Jahar Tamu Mai Albarka Jihar Kebbi.

Bakin Cikinsu Shine Mai Girma Gwamna Yayi Abunda Bazasu iyaba Na Kawo Cigaba Cikin Ƙanƙanin Lokaci A Ƙasa Da Shekara Biyu. Tunda Aka Kirkiri Jihar Kebbi A 1991 Munyi Gwamnoni Daban-Daban Amma Babu Kamar Kauran-Gwandu Wannan Shine Baƙin Cikinsu.

Kusani Hakarku Bazata Cimma Ruwa Cewar Hon. Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa, Kuma Insha Allahu Zamu Ɗauki Mataki Akan Wannan Abu. Bazamu Lamuncin irin Wannan Cin Mutuncin Da Kazafi Da Akeyima Mai Girma Gwamnaba.

Zamu Duƙufa Wajen Gano Waɗannan Mutanen Dasuka Ɗauki Aniyar Kawo Hargitsi Cikin Jihar Kebbi Da Jam'iyyar APC, Zamu Dauki Ƙwaƙƙwaran Matakin Daya Dace Akansu.

Jihar Kebbi Ta APC Ce Kuma Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Na Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Ne. Kauran-Gwandu Da Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Zaɓin Allah Ne.

Duk Abunda Akeyi Na Cigaba Mai Girma Gwamna Da Shugaban Ƙasa Sunyi Munashi.

Daga Ƙarshe Ƴan-Tagwayen Kangiwa Yayi Addu'ar Allah Ya Ƙaraba Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris ("Kauran-Gwandu") Da Shugaban Ƙasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu Nasara Suci Gabada Kawo Cigaba Cikin Jiharmu Ta Kebbi Da Najeriya Baki Ɗaya.

Follow Us