"YAN BINDIGA SUN SHA KASHI A KOKARIN SHIGA DAN MUSA.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06052025_091602_Nigerian-Military-begins-probe-into-video-of-terrorists-holding-peace-meeting-with-soldiers-in-Katsina-2.jpg

Daga wakilanmu  @ Katsina times 

Yan Bindiga Sun yi kokarin Shiga karamar Hukumar Danmusa, ajiya Litinin 05 05 2025 lamarin ya faru ne Da misalin karfe 11 na dare.

Wasu mazauna Garin da muka samu zantawa dasu a wayar salula sun bukaci a saka Sunan su sun  bayyana mana cewa, tunda 11:00pm na dare jami'an tsaro ke dauki ba dadi tsanin su da barayin dajin har wajen karfe 4:30 na safe, ranar talatar nan da muke ciki.

Sun tabbatar mana da cewa sun sace  wasu mutane wadanda har yanzu baa San ko mutum nawa bane.

Majiyar mu ta tabbatar mana da kashe wani Babban Dan ta'adan dajin Wanda shi ya jagoranci shigowa cikin garin Danmusa Mai suna malam Wanda na Daya Daga cikin Wanda ya addabi yankin Danmusa da kankara da Safana har ma da yankin yankin Zamfara

Sai da yan bindigar Sunyi ajalin Wata mata aure, sun kuma ji wa wasu matan rauni.
Kwamishinan tsaro na jahar Katsina, Alhaji Nasiru Muazu Dan musa ya tabbatarwa da jaridun Katsina times da faruwar lamarin.
Kwamishinan ya nuna jinjina da godiya ga jami an tsaron da suka fafata da wàdannan miyagun kuma suka yi masu barna da hana su mugun nufin shigowa Dan musa don aikata ta addancinsu.

Alhaji Nasiru ya tabbatar mana an kashe wani mugun  Dan ta adda wanda shine shugaban ISWAP a yankin.

Da Musa yayi jinjina ga mutanen gari Dan musa da suke ba jami an tsaro hadin kai da fahimtar yadda suke aikinsu.

Follow Us