Shugaban Hukumar Raya Ci-gaban Kasashen Afrika ta Yamma (AUDA-NEPAD), Hon. Jabiru Salisu Tsauri, tare da Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, sun halarci bikin kaddamar da jirgin farko na aikin Hajjin 2025 a jihar Imo.
An gudanar da bikin ne a ranar Jumu’a, 9 ga Mayu, 2025, a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Owerri, babban birnin jihar Imo, inda aka kaddamar da jirgin farko na mahajjata zuwa ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.
Bikin ya samu halartar fitattun baki daga sassa daban-daban na ƙasa, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma.
Sauran manyan baki da suka halarta sun hada da Sheikh Saleh Pakistan, Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa; Hajiya Olubunmi Kuku, Babbar Darakta kuma Shugabar Hukumar FAAN; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III; da Sanata Abubakar Sani Bello, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Ƙasashen Waje.
Yayin da mahajjatan ke shirin tafiya domin aiwatar da ibadar Hajji, ana addu’ar Allah Ya kiyaye su, Ya sauƙaƙa musu tafiyar, kuma Ya karɓi ibadarsu. Allah Ya albarkaci hajjin bana, ayi lafiya a tafi, a gama lafiya.