Kungiyar Red cross a Katsina ta gudanar da gangamin "Ranar Bada Agajin Gaggawa" ta duniya.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_201911_FB_IMG_1746819346750.jpg



Daga Auwal Isah Musa 

Kungiyar bada agajin gaggawa ta duniya a Nijeriya, reshen jihar Katsina (Red cross) ta bi sauran danginta wajen gudanar da taron gangamin "Ranar Bada Agajin Gaggawa Ta Duniya" a jihar ta Katsina.

A yayin taron gangamin, membobin kungiyar sun yi kwarya-kwaryar zagaye a birnin na Katsina, inda suka fara daga kofar kaura zuwa sha-tale-talen kofar marusa, suna dauke da Banoni masu alamata ranar tasu da abin da kunsa tare da rarraba kunshin sakon rubutu (Article).

Da yake zantawa da wakilan jaridun KatsinaTimes a yayin gangamin, magatakardar kungiyar na jihar ta Katsina, Bala Abdullahi Husaini ya bayyana yadda kungiyar a fadin kasashen duniya sama da 100 ke gudanar da gangamin "domin nuna damuwa da jajantawa wadanda Ibtila'o'i daban ya shafa" a bana.

Hakazalika, Bala Abdullahi ya bayyana irin aikace-aikacen da kungiyar ta aiwatar a ranar farko na zagayowar ranar tasu a jihar, wanda suka fara a ranar Alhamis din nan, inda suka ziyarci gidajen marayu; suka tallafa masu da abinci da abubuwan bukatun yau da kullum, sannan ya bayyana shirinsu na zuwa wasu makarantu a cikin makon nan inda za su koya masu yadda ake bada taimakon gaggawa(First Aid).

Dangane da wasu nasarorin da kungiyar ta samu a matakin jihar, Bala ya bayyana irin rawar da Red cross din ta taka musamman na kai gudummmuwar zunzurutun kudade sama da miliyan 124 ga kananan hukukomin Kurfi, Katsina da jibiya wadanda Ibtila'in 'yanbindiga ya shafa a shekaru biyu da suka gabata.

Sauran nasarorin da kungiyar ta samu, a cewarsa, sun hada da: yarda da karbuwar da kungiyar samu daga al'umma; da ayyukan wayar da kan al'umma da kungiyar ke yi game da cututttuka kamar mashako, amai da gudawa, da Ibtila'in ambaliyar ruwa, Gobara, kula da asibitoci da marasa lafiya a lokacin yajin aiki ko bukukuwan Sallah da Maulidi, da buda hanyoyi idan gari ya cunkushe, da kuma bada horo da horarwa ga fararen hula har ma da jam'ian tsaro da sauransu game da taimakon gaggawa, kare kai da kuma yadda za a fitar da kai idan wani hadari ya afku.

Har wa yau, Bala ya bayyana kalubale ko matsalolin da suke fuskanta, inda ya bayyana rashin samun mazauni da din-din-din isasshe don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, da kuma ababen hawa na musamman don shiga wuraren masu nisa suka kai makon gaggawa kan kari idan bukatuwar hakan ta taso.

Daga karshe ya a yaba tade da godewa gwamnatin jihar Katsina game da irin taimakon da take ba su ta bangarori da dama a duk lokacin da suka bukaci hakan, inda ya bayyana hatta matsugunnin da kungiyar ke amfani da shi a matsayin gwamnatin ce ke daukar nauyin biya masu kudin hayarsa "duk da cewar kungiyar Red cross ba ta siyasa ko wani bangare a cikin bangarorin addini ba ce." In ji shi.

A duk ranar 8 ga watan mayu na kowace shekara, kungiyar ta Red Cross na gudanar da gangami a kasashen sama da 100 na duniya, domin kara wayar da kan jama'a game da ayyukan kungiyar na jinkai da taimako, gami da tunawa da ranar haihuwar wanda ya yi tunanin samar da kungiyar, Henry Dunat.

Kungiyar Red Cross dai an kafa ta ne a shekarar 1859 domin taimakwa wajen samar da taimako ga wadanda suka jikkata a lokacin yaki, bayan bukatuwar hakan da wani dan kasuwar kasar switzerlanda mai suna 'Henry Dunant' ya gabatar, a yayin bada bayanin abin da ya wakana mai taken "Tunawa da yakin Solferino" biyo bayan abin da ya gani da idonsa na wani kazamin yaki da ya faru kasar Italy, inda bayan tattaunawa aka amince da ita da samar mata tambari, inda aka rika canja shi a wasu mabambantan lokutta.

A shekarar 1960, Nijeriya ta amince da kungiyar ta Red cross domin tallafawa da taimakawa mutane wadanda wani Ibtila'i ya afka masu, da kuma shirye-shiryen kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa da yada akidar jinkai a kasar.

Follow Us