KEDCO ta ce Masana’antun Challawa na samun wuta na tsawon awanni 23 da mintuna 45 a kullum
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya musanta zargin da kungiyar masana’antun Challawa ta yi dangane da rashin wadatar wutar lantarki da kuma tsadar farashin wuta da ake ci a yankin masana’antu na Challawa da ke jihar Kano.
Wannan martani ya biyo bayan zantawar da Sakatare na kungiyar masana’antun Challawa, Aliyu Mahadi, ya yi a tashar Channels TV, yayin da tawagar NDPHC da NASENI suka kai ziyara zuwa yankin masana’antun a Kano. A cewar KEDCO, zargin ya kasance cike da ƙarya da yaudara, kuma dole ne kamfanin ya fito fili ya bayyana gaskiya.
A cewar bayanan kididdiga daga tsarin aika bayanan kamfanin, wutar lantarki da ake bai wa masana’antun da ke Challawa – ciki har da 33kV Coca Cola, 11kV Ceramic, da 11kV NBC – dukkan su na Band A, sun rika samun matsakaicin wuta na tsawon awanni 23 da mintuna 45 a kullum tun kafin ma rahoton.
KEDCO ta kuma karyata ikirarin da ke cewa an saka su a Band C, tana mai cewa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) tana da cikakken iko da lura da matsayin ayyuka da compliance na kamfanonin rarraba wuta. Idan da zargin ya kasance gaskiya, an riga an sauke su daga Band A zuwa Band C bisa tanadin dokar yarjejeniyar sabis.
Kamfanin ya bayyana cewa burinsa shi ne samar da wutar lantarki mai inganci ga kowanne gida da kamfani da ke karkashin yankinsa. Ya ce yana bai wa wuraren masana’antu kamar Challawa fifiko, musamman saboda rawar da suke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da ayyukan yi.
A cikin watanni 12 da suka gabata, KEDCO ta ce ta dauki matakai na rage wa kamfanoni da masana’antu nauyin hauhawar kudin wutar lantarki ta hanyar samar da ingantacciyar wuta da kudin da ya fi rahusa kasa da farashin kasuwa. Wannan, in ji kamfanin, zai taimaka wajen habaka kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi.
Daga karshe, KEDCO ta shawarci abokan cinikinta da su rika bincike da tantance gaskiyar lamurra kafin su yanke hukunci ko su yada bayanai da ka iya bata sunan kamfanin da martabarsa. Ta jaddada kudurinta na ci gaba da inganta ayyuka ta hanyar zuba jari a fannin fasaha da fadada cibiyoyin wuta don rage asara da kara inganci.