Rashin Biyan Albashi da Maƙarƙashiyar Daukar Ma’aikata a BLEA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21052025_222247_FB_IMG_1747866113286.jpg


Daga wakilanmu | Katsina times 

Malaman Firamare na Bakori Sun Bukaci Gwamna Radda Ya Shiga Tsakanin Lamarin
Malaman makarantar firamare a ƙarƙashin Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Bakori (BLEA) sun sake yin ƙorafi kan abin da suka bayyana a matsayin cin zarafi da karɓar albashi ba bisa ka’ida ba, da kuma wata sabuwar matsala da ke ƙara dagula sha’anin ilimi a yankin.

Malaman sun zargi hukumar da rashin adalci wajen biyan albashi, inda a cewarsu, kowanne wata ana zaɓar wasu daga cikinsu a bazata a hana su albashi ko a cire wani kaso na albashinsu ba tare da wani bayani ba. Wasu sun ce suna shafe watanni biyu zuwa uku ba tare da an biya su albashi ba, kuma ko da an dawo da biyan, kuɗin da aka rasa baya dawowa. Dukkan ƙoƙarin da suka yi wajen neman mafita — ciki har da kai ƙorafi ga shugaban ƙasa da kungiyar malamai — sun ci tura.

A cewarsu, abin da ya fi ba su mamaki shi ne yadda albashin da ake biya daga gwamnatin jihar kai tsaye ke samun cirewa ko hanawa ba tare da bayani ko tushe na doka ba. Malaman sun roƙi Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, da ya shiga tsakani domin ceto su daga wannan zalunci.

Sai dai wani sabon bayani ya bayyana cewa matsalolin da ke addabar BLEA ba a tsaya ga rashin biyan albashi kaɗai ba. Rahotanni sun nuna cewa akwai malamai da dama — musamman mata — waɗanda ke cikin jerin masu albashi amma sun bar bakin aiki tun shekaru da dama da suka bi mazajensu zuwa wasu sassan ƙasar.
Wadannan malamai sun kulla yarjejeniya da matasa marasa aikin yi don su dinga koyarwa a madadinsu, inda suke biyansu kuɗin alawa.

Wannan shirya-shirye ana yinsu ne da haɗin guiwar wasu daga cikin jagororin Hukumar Ilimi ta Bakori, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
“Akwai malamai da dama da suka bar aikin fiye da shekaru uku da suka gabata, amma har yanzu suna karɓar albashi kamar suna nan,” inji wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.

Wannan al’amari na kara tayar da hankula musamman ganin yadda dubban matasa da suka kammala karatu ke zaman kashe wando ba tare da samun aikin koyarwa ba.

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnatin jihar da ta yi bincike mai zurfi kan yadda ake tafiyar da harkokin albashi da ma’aikata a BLEA, tare da daukar matakan ladabtarwa ga dukkan masu hannu a cikin wannan badakala.
“Wannan matsala ta cin zarafi da karya doka ba wai kawai na tauye hakkin malamai bane, har ma yana barazana ga ingancin ilimi da makomar yara a Bakori,” inji wani malamin da ke cikin waɗanda abin ya shafa.

Yayin da ake ci gaba da jiran matakin da gwamnatin jihar za ta dauka, malamai da mazauna yankin na fatan za a kawo ƙarshen wannan danyen aiki domin kare martabar aikin koyarwa da rayuwar ɗalibai.
Munyi kokarin magana da sakataren ilmi na karamar hukumar Bakori bai dauki waya ba, bai kuma maido da amsar sakon rubutu da muka aika masa ba.

Follow Us