Hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda wata mahajjaciya daga jihar Zamfara ta ketare tantancewar daukar ciki, inda ta isa kasa mai tsarki kuma ta haifi jariri a can.
Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike da Bayanai na Hukumar, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da 'yan jarida a birnin Madina.
Yagawal ya ce NAHCON za ta tuntubi masu kula da harkokin hajji na jihohi domin tabbatar da cikakken bincike, musamman ga mata, don kare rayukansu da na jariran da ke cikinsu.
Ya jaddada cewa bai kamata a dora wa hukumar jin dadin alhazai ta jiha ko ta kasa cikakken laifi ba dangane da abin da mahajjaciyar ta aikata.
“Kodayake ba ina kare hukumar jin dadin alhazai ta kowace jiha ba ne, amma akwai wasu dalilai da ka iya haddasa irin wannan kuskure,” in ji shi.
Game da ayyukan bata gari na masu damfara da barayin kudi, musamman a Madina, Yagawal ya ce jami’an hukumar za su ci gaba da wayar da kan alhazai kan matakan kariya.
“Abin takaici ne kuma abin kunya ga Musulmi ya nuna rashin tausayi har ya aikata wadannan laifuka a kasa mai tsarki.