Najeriya Za Ta Karɓi Bakin Taron UN Na 68 Kan Yawon Buɗe Ido Na Afirka a 2025

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01062025_173207_FB_IMG_1748798765925.jpg

Najeriya Za Ta Karɓi Bakin Taron UN Na 68 Kan Yawon Buɗe Ido Na Afirka a 2025


Najeriya ta samu tabbacin zama mai masaukin baki na taron karo na 68 na Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Majalisar Ɗinkin Duniya (CAF 2025), bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka yi a birnin Madrid tsakanin Ministar Harkokin Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Kirkira, Barista Hannatu Musa Musawa, da Sakatare-Janar na UN Tourism, Zurab Pololikashvili.

An shirya gudanar da taron daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Yuni, 2025, inda za a tattauna kan jigon taron mai taken: “Ƙarfafa Tasirin Jama'a da Ilimi a Fannin Yawon Buɗe Ido ta Hanyar Kirkire-kirkire, AI da Masana'antar Fasaha.”

A yayin bikin rattaba hannun, Minista Musawa ta bayyana taron a matsayin wata dama ta musamman don ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe da kuma inganta ci gaban yawon buɗe ido mai ɗorewa. Ta kuma tabbatar da shirin Najeriya na karɓar bakuncin taron, tare da jaddada irin fa’idar tattalin arziki da al’adu da taron zai haifar.

Ana sa ran taron CAF 2025 zai haskaka matsayin Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan wuraren yawon buɗe ido da ke amfana da sabbin fasahohi da ƙirƙira a nahiyar Afirka.

Shirye-shirye sun fara kamar yadda Najeriya ke ci gaba da tsarawa don tarbar manyan jami’an yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya a shekarar 2025.

Follow Us