A ranar litinin 02-06-2025 kungiyar Climate Adaptation and Resilience in Tropical Drylands (CLARITY) ta shirya taron na yini daya a dakin taro na Hillside dake cikin garin Katsina.
Da yake gabatar da jawabin sa shugaban kungiyar Prof. Ibrahim Goni ya bayyana cewa" wannan shiri kasashen UK da Canada ne suka dauki nauyin sa.
Domin zuwa a tattauna da mutane wanda sauyin yanayi ya shafa musamman karancin ruwa da zafi domin a zauna dasu a fahimtar, tare da basu ilimin yadda zasu yi amfani da abinda suke dashi ta yadda ya da dace.
A kuma shigo da sassa na hukumomin gwamnati ciki domin ganin irin rawa da gudunmuwar da zasu bada a aikace zuwa ga wadannan al'umma.
Shima a nasa jawabin kwamishinan ma'aikatar ruwa na jihar Katsina wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar Alh. Aminu Dambo Ingawa ya yaba matuka ga wanda suka kawo wannan shiri a jihar Katsina.
Tare da bayyana wasu daga cikin irin shir da tsare tsaren da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Mal. Dikko Umar Radda ta keda shi a wannan fanni domin ciyar da al'umma gaba.
Shima a nasa jawabin na sa albarka mai martaba sarkin Katsina wanda ya samu wakilcin sarkin Fulani Hamcheta ya yaba matuka akan shiri tare da bayyana aniyar masaurata naba wannan shiri ko wace irin gudunmuwa matsayin su na iyayen al'umma.
Prof. Yagana Bukar itace babbar bakuwa da gabatar da kasida a wurin taron, sai kuma Engr. Abdullahi Bello wanda shima yasa albarka kuma yayi tsokaci.
Wasu daga cikin mahalta taron daga bangarori daban daban na jihar Katsina sun nuna jin dadin su bisa wannan shiri da suka zo tare da kara nuna jin dadin su akan ilimin da suka samu wanda a baya basu da shi.
Shugaban hukumar kula da kasa a taswirance KATGIS Alh. Mansir Aminu shine ya kaddamar da bude taron na yini daya a madadin gwamnatin jihar Katsina.
Taron ya samu halartar shugaban hukumar STOWASSA ta jihar Katsina, wakilin shugaban hukumar samar da ruwa ta jihar Katsina, wakilin kwamishinan kasa da safiyo na jihar Katsina.
Wakilin hukumar yan sanda ta kasa, wakilin hukumar fararen kaya ta jihar Katsina da dai sauran su.