Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES
Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da bikin karrama Malam Mustapha Zubairu, tsohon Sakataren Dindindin na Sashen Harkokin Siyasa, a wani taron bankwana da aka gudanar a ranar Talata, 3 ga Yuni, 2025 a sakatariyar jihar.
Taron, wanda Sakataren Gwamnati, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya jagoranta, ya kasance dama ta nuna godiya da yabon kokarin Malam Mustapha Zubairu wajen gudanar da ayyukansa na gwamnati da kwarewa. Faskari ya bayyana Zubairu a matsayin gwarzon ma’aikaci mai gaskiya, amana da jajircewa, yana mai fatan alheri a gare shi da sauran ma’aikatan da ke kan aiki.
A jawabinsa na ban kwana, Malam Mustapha Zubairu ya mika godiya ga daukacin ma’aikata bisa hadin kai da goyon bayan da ya samu a lokacin da yake kan aiki. Ya kuma yi fatan nasara ga sabon Sakataren Sashen "Cabinet and Security" Alhaji Aminu Tukur da sauran abokan aiki.
Haka kuma, sabon Sakataren Dindindin na Sashen (Cabinet and Security,)Alhaji Aminu Tukur, da Daraktan Mulki sun bayyana Mustapha Zubairu a matsayin shugaba nagari, wanda ya sadaukar da kansa don ci gaban ma’aikata da ayyukan gwamnati.
A wannan rana, an kuma samu sauyin jagoranci a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Katsina, inda Geologist Aminu Tukur, wanda ya jagoranci ma’aikatar na tsawon shekara guda da wata goma sha ɗaya, ya mika ragamar shugabanci ga Alhaji Ibrahim Dasuki, tsohon Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina.
Aminu Tukur ya bar tarihi mai kyau a lokacin da yake jagoranci, inda aka samu ci gaba a ayyuka da dama na ma’aikatar. An yaba masa da irin jajircewa, gaskiya da mutunta kowa da kowa, wanda hakan ya sanya ma’aikata da dama jin kewarsa tare da hawaye a yayin bankwana.
Yanzu haka, Aminu Tukur ya kama sabuwar mukaminsa a Ofishin Sakataren Gwamnati a matsayin Sakataren Dindindin na Cabinet and Security, yayin da Alhaji Ibrahim Dasuki zai ci gaba da jagoranci a matsayin mukaddashin Sakataren Dindindin har zuwa dawowar Alhaji Hamza Umar Tafashiya daga aikin Hajji a Saudiyya.
Jama’a da dama sun yaba da wadannan sauye-sauyen da gwamnatin Jihar Katsina ke aiwatarwa, inda suka jinjina wa Gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa jajircewarsa na inganta shugabanci da karrama kwararrun ma’aikata. Wannan ya nuna sabuwar manufa ta dorewar ci gaba da ingantacciyar tafiya a harkokin ma’aikata da sassa daban-daban na gwamnati.